Durbar: Kotu ta soma ba iyalin Janar Abacha gaskiya a shari’arsu da Gwamnatin El-Rufai

Durbar: Kotu ta soma ba iyalin Janar Abacha gaskiya a shari’arsu da Gwamnatin El-Rufai

  • Ana shari’a tsakanin lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna da na masu kamfanin Durbar hotel PLC
  • Lauyoyin Durbar hotel sun yi kuskure wajen rubuta sunan hukumar KASUPDA a shari’ar da ake yi
  • A kan wannan lauyoyin gwamnati su ka samu dama, su ka fake da shi a kotu har aka yi zama a yau

Kaduna - A ranar Litinin, Alkali Hannatu Balogun ta babban kotun jihar Kaduna ta yi zama a kan batun shari’ar Durbar hotel Plc da gwamnatin jihar Kaduna.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar 4 ga watan Afrilu 2022, ta ce Mai shari’a Hannatu Balogun ta ki karbar uzurin da aka bada na wani tuntuben sunan da aka yi.

Kotu ta ce sanya Kaduna State Urban Planning & Development Agency maimakon Kaduna State Urban Planning & Development Authority bai canza komai ba.

Kara karanta wannan

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Hannatu Balogun a hukuncin da ta zartar, ta ce kuskuren suna ne kurum aka yi a shari’a, kuma duk wani mai tunani ba zai ce an batar da shi saboda kuskuren ba.

"Duk mai hankali a Kaduna zai dauka Kaduna State Urban Planning and Development Agency ake nufi da Kaduna State Urban Planning and Development Authority."

Rahoton ya ce Alkali ta daga karar sai zuwa ranar 5 ga watan Yuli 2022 domin sake sauraron shari’ar.

Durbar Hotel PLC
Durbar Hotel a Kaduna Hoto: www.agoda.com
Asali: UGC

Babu wannan hukuma a Kaduna?

Lauyan gwamnatin Kaduna, S. S Umaru ya fadawa kotu a zaman da aka yi, ba a san da zaman wata Kaduna State Urban Planning and Development Agency ba.

Amma babban lauyan da yake kare masu kamfanin Durbar hotel, Dr. Reuben Atabo ya ce sun roki kotu dama domin a gyara kuskuren da aka yi wajen rubuta sunan.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Samuel Katung ya wakilci Reuben Atabo

Samuel Katung (SAN) ne ya wakilci Dr. Reuben Atabo (SAN) a zaman yau, kuma ya shaidawa manema labarai yadda ta kaya a kan gardamar kuren sunan hukumar.

Samuel Katung ya ce kafin dokar KASUPDA ta shekarar 2015, an san wannan hukumar ne Kaduna State Urban Planning and Development Agency (KASUPDA).

A kan wannan tuntuben alkalami, lauyan gwamnati ya nemi ayi fatali da kararsu. Amma a karshe kotu ta ce kuskuren da aka yi bai canza komai wajen shari’a ba.

Alkali ta daga karar zuwa ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2022 domin a cigaba da sauaron karar.

Shari'ar da aka yi a Kotu

Kwanaki kun ji labari cewa iyalan Janar Sani Abacha sun bukaci kotun jihar Kaduna ta umurci Gwamna Nasir El-Rufai ya biya su N11.7bn a dalilin ruguza masu otel.

Wadannan Bayin Allah su na neman wannan kudin ne a matsayin diyya a kan ikirarin da su ka yi na cewa El-Rufai da wasu jami'an gwamnatinsa sun rusa masu otel.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Asali: Legit.ng

Online view pixel