Hukumar NDLEA ta bukaci a hana cire kudi daga asusun bankin Abba Kyari

Hukumar NDLEA ta bukaci a hana cire kudi daga asusun bankin Abba Kyari

  • An bukaci gwamnatin tarayya ta bada umurnin hana cire kudi daga asusun bankin DCP Abba Kyari da abokan harkallarsa
  • Hukumar hana fasa kwabri da ta'amuni da kwayoyi NDLEA ne ta mika wannan bukata ga ofishin Antoni Janar na tarayya
  • A cewar masu binciken NDLEA, mafi akasarin kudin dake asusun bankin Abba Kyari daga harkar kwayoyi ya samesu

Bayan gurfanarsa a babbar kotun tarayya dake Abuja ranar Litinin, 14 ga Maris, Abba Kyari, ya shiga sabon tasku da hukumar hana fasa kwabri da ta'amuni da kwayoyi NDLEA.

NDLEA ta bukaci gwamnatin tarayya ta daskarar da asusun bankin Abba Kyari da abokan harkallarsa dake tsare.

Vanguard ta ruwaito cewa jami'an dake binciken alakar dake tsakanin Abba Kyari da masu safarar kwayar da aka kama a tashar jirgin Enugu da Legas sun samu makudan miliyoyi a asusunsa.

Kara karanta wannan

Tserewa zai yi: NDLEA ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari, an dage kara

Abba Kyari
Hukumar NDLEA ta bukaci a hana cire kudi daga asusun bankin Abba Kyari Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Rahoton yace masu binciken sun samu miliyoyin Nairori, daloli da fam a asusun Abba Kyari da sauran abokan harkallarsa.

A cewarsu, ana zargin sun tara wadannan kudade ne ta hanyar harkalla da masu safarar kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel