Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Nairobi, kasar Kenya don halartan taron murnar cikar shirin majalisar dinkin duniya na yanayi shekaru 50 (UNEP@50).

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, yace an shirye yin taron ranar 3-4 ga Maris, 2022.

Adesina yace Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanayi, Sharon Ikeazor; NSA Manjo Janar Babagana Monguno; DG na NIA, Ambasada Rufai Abubakar, da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Dirarsa ke da wuya, Shugaba Buhari ya gana da Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta.

Kalli hotunan lokacin da ya dira Nairobi:

Asali: Legit.ng

Online view pixel