Zamfara: Ƴan Sanda Sun Ceto Jinjira Ƴar Wata 7, Mata Masu Shayarwa Da Wasu Mutane 21 Daga Hannun Ƴan Ta’adda
- Jami'an tsaro a Jihar Zamfara sun kai samame mafakar yan bindiga sun ceto mutum 24 kauyen Gurgurawa a karamar hukumar Bungudu
- Bayan musayar wuta da yan bindigan, jami'an tsaron sun yi nasarar ceto mutum 24 cikinsu da jinjira yar wata bakwai, maza, mata da mata masu shayarwa
- Tuni dai jami'an tsaron sun sada wasu daga cikin mutanen da aka ceto da yan uwansu bayan an musu tambayoyi an kuma duba lafiyarsu an tabbatar kalau suke
Jami'an yan sanda a Jihar Zamfara sun ceto mutane 24 da masu garkuwa suka kama su ciki harda jinjiri dan watanni bakwai, mata masu shayarwa bayan musayar wuta da yan bindiga a jihar.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa jami'an yan sandan na musamman da aka tura kauyen Gurgurawa a karamar hukumar Bungudu ne suka yi nasarar ceto mutanen.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a hedkwatar yan sanda a Gusau, da yammacin ranar Asabar, kakakin yan sanda, SP Muhammad Shehu, ya ce 'an ceto dukkan wadanda aka yi garkuwa da su'.
Shehu ya ce likitoci sun kammala duba mutane 11 cikin wadanda aka ceto, an musu tambayoyi an kuma mika su ga yan uwansu, rahoton Nigerian Tribune.
Ya ce:
"An sace su ne a lokacin da yan bindigan suka kai hari a garuruwansu a ranar Juma'a da dare sannan suka sace wasu mutanen da dama daga garin.
"An ceto mutane ashirin da hudu yayin da jami'an tsaron suka yi musayar wuta da yan bindigan, wata mace ta yi rauni kuma a yanzu ana mata magani a asibitin jihar."
"Cikin wadanda aka ceto akwai wata jinjira yar watanni bakwai, maza, mata da mata masu shayarwa."
Sojojin Najeriya Sun Yi Raga-raga Da Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara
A wani labarin, Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation Hadin Kai ta lalata sansanin ‘yan bindiga da ke dajin Totsari da Kenkashi a karamar hukumar Tsafe cikin Jihar Zamfara.
A ranar Laraba wata majiya cikin mazauna Mada ta sanar da Channels TV cewa a ranar Talata rundunar Operation Hadin Kai ta kai samame kauyen Getawa, Unguwan Kade da kauyen Maigalma inda ta ci karo da ‘yan bindigan sun koro shanun da suka sace.
Asali: Legit.ng