Daga haduwa a Facebook: Wani ya ci duka saboda neman kulla soyayya da matar dan siyasa

Daga haduwa a Facebook: Wani ya ci duka saboda neman kulla soyayya da matar dan siyasa

  • An nadawa wani magidanci mai suna Andrew Lee Oscar na jaki kan zargin kokarin haduwa da matar wani dan siyasa
  • Oscar dai ya hadu da matar ne a shafin soshiyal midiya inda suka fara hira har ya nemi su hadu
  • Bayan matar ta sanar da mijinta halin da ake ciki, sai suka shirya masa gadar zare inda shi kuma ya afka

Wani magidanci mai suna Andrew Lee Oscar ya sha na jaki kan zargin hira da matar wani dan siyasa a jihar Delta a kan shafin Facebook, sannan ya nemi kulla soyayya da ita.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Victor Kelechi Onyendi, wanda shine ya wallafa labarin ya ce wacce mutumin ke hira da ita ta kasance matar Hon. Precious Ajaino, darakta janar na kwadago kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ethiope ta yamma.

Kara karanta wannan

Dalibi ya dirka wa malamar shi ciki, ta ce ba zata zubar ba

Daga haduwa a Facebook: Wani ya ci duka saboda neman kulla soyayya da matar dan siyasa
Daga haduwa a Facebook: Wani ya ci duka saboda neman kulla soyayya da matar dan siyasa Hoto: Victor Kelechi Onyendi
Asali: Facebook

An tattaro cewa magidancin ya nemi ya kulla soyayya da matar kafin ita da mijin nata suka shirya yadda za su kama shi.

Onyendi ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A nan hotunan Andrew Oscar Lee ne. labarin shine cewa Oscar ya yi wata hira da matar Hon. Precious Ajaino, darakta janar na kwadago kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ethiope ta yamma, jihar Delta.
“Oscar ya nemi haduwa da matar auren ta shafin Facebook, sai matar ta bayyanawa mijinta hirar da suka yi da shi, sannan sai ma’auratan suka shirya wa Oscar gadar zare.
“Wasu matasa da Hon. Ajaino da matarsa suka yo haya sun farma Oscar sannan suka yi masa dukan tsiya, kafin aka mika sa ga yan sanda.”

Wata Sabuwa: Kotu ta datse igiyoyin aure kan zargin mijin ya faɗa soyayya da kare

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

A wani labarin, wata yar kasuwa, Rashidat Ogunniyi, wacce ke tuhumar mijinta da nuna soyayya da kula ga karensa fiye da ita, ta samu abin da take nema a kotu.

Premium Times ta ruwaito cewa wata kotun Kwastumare dake zamanta a jihar Legas, ta datse igiyoyin auren mutanen biyu.

Akalin kotun, mai shari'a Adeniyi Koledoye, ya bayyana cewa rashin halartar wanda ake zargi zuwa kotun ba zai hana cigaba da sauraron Shari'ar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel