Kaduna: Ƴan Bindiga Da Suka Kawo Hari Sun Ji Ba Daɗi Hannun Jami’an Tsaro, Guda Cikinsu Ya Baƙunci Lahira
- Wani dan ta’adda ya halaka yayin da jami’an tsaro suka mayar da hari da ‘yan bindiga suka kai Hayin Gada da ke gundumar Shika a Karamar hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna
- An samu bayanai dangane da yadda ‘yan bindiga suka afka yankin a ranar Juma’a da misalin karfe 11 na dare inda suka yi kacibus da jami’an tsaro
- ‘Yan bindiga suna ci gaba da addabar karamar hukumar Giwa cikin dan datsin nan, sai dai wannan karon Ubangiji ya kai wa mutanen yankin dauki da gaggawa
Jihar Kaduna - Daya daga cikin ‘yan ta’addan da suka kai hari Hayin Gada da ke gundumar Shika a karamar hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna ya rasa ransa.
Daily Trust tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan suka kai farmaki yankin a ranar Juma’a.
‘Yan ta’addan sun isa Hayin Gada ne da misalin karfe 11 na daren Juma’a amma ba su samu sa’a ba, sai suka yi kacibus da jami’an tsaro a yankin.
Karamar hukumar Giwa tana ci gaba da fuskantar ta’addanci cikin ‘yan kwanakin nan.
Daily Trust ta gano cewa ‘yan ta’addan sun addabi yankin ne bayan an kara yawan jami’an tsaro a Jihar Zamfara da Katsina.
Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Cibiyar Bincike akan Samar da Dabbobi ta kasa, NAPRI, da gidajen ma’aikatan cibiyar da na ma’aikatan ABU suna da yawa kwarai a gundumar Shika.
Jami’an tsaro sun halaka dan ta’adda daya sannan sun ceto wani ma’aikacin NAPRI da yaran sa biyu
Majiyoyi sun tabbatar da yadda daya daga cikin ‘yan bindigan ya rasa ran sa yayin musayar wuta da jami’an tsaro inda ya yi kokarin guduwa.
Jami’an tsaron sun samu nasarar ceto wani ma’akacin NAPRI, Shika, Mr Katung da yaran sa biyu.
'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida
A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.
Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.
Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.
Asali: Legit.ng