Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC

Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC

Birnin FCT, Abuja - Hukumar lura da man fetur na kasa NMDPRA, a ranar Laraba ya bayyana cewa akalla jiragen ruwa guda shida jibge da man fetur sun dira Najeriya.

Shugaban hukumar NMDPRA, Farouq Ahmed, ya bayyana cewa jiragen ruwan na dauke da lita milyan 300 na man fetur kuma zai taimaka wajen dakile tsadar man dake faruwa yanzu musamman a biranen Abuja da Legas.

Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC
Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC
Asali: UGC

Ahmed yace hukumarsa ta samu nasarar hada kai da manyan yan kasuwan mai wajen magance matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Yau, ina farin cikin fadin cewa ana lodin mai a depot saboda sun samu damar killace gurbataccen man da aka kawo Najeriya."

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

"Jiragen ruwa sun dira Najeriya kwanan nan. Akalla guda shida da NNPC tayi oda dauke da litan mai milyan 300 sun iso."

A cewarsa, Najeriya na da isasshen mai da zai isa na tsawon kwanaki 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel