Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje

Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ba zai bata lokaci wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko ba idan kotu tayi hakan.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyayen Hanifa Abubakar a gidansu dake Dakata/Kawaji.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Dr Nasiru Gawuna; shugaban masu rinjaye a majalisar jihar, Labaran Abdul Madari; da wasu manyan jiga-jigan gwamnati.

Yace:

"Mun samu labarin cewa kotu zata tabbatar da anyi adalci. Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba."
"Kundin tsarin mulkinmu ya bukaci cewa idan an yanke hukuncin kisa, gwamna na da karfin rattafa hannu a kashe mai laifi. Ina tabbatar muku cewa ba zan bata lokaci ko dakika guda ba."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

"Gwamnati zata kula da iyalan 'yarmu marigayiya Hanifa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje
Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel