Babu lantarki, babu kayan wuta, ta yaya wuta ya tashi: Zulum kan gobarar sabuwar makarantar da ya gina
- Farfesa Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno ya yi zargin cewa akwai lauje cikin nadi game da gobarar da ta lashe makarantar sakandare ta Muna
- Zulum ya ce akwai matukar daure kai da mamaki a samu gobara a makarantar da Shugaba Buhari ya kaddamar duk da cewa babu lantarki ko janareta a makarantar
- Gwamnan na Borno ya ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna akwai yiwuwar zagon kasa kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba sai an gano sababin gobarar
Borno - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin akwai zagon kasa a yayin da gobara ta lashe babban makarantar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Borno kimanin watanni shida da suka gabata.
Da ya ke magana a harabar makarantar da ke Muna a Karamar Hukumar Jere na jihar, a ranar Talata, gwamnan ya ce akwai matukar mamaki a ce makarantar da babu wutan lantarki ta kone, rahoton The Punch.
Za mu gudanar da bincike don gano abin da ya faru, Zulum
Ya ce gwamnatinsa za ta gudanar da bincike domin gano musababbin afkuwar gobarar.
Zulum ya ce:
"Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da makarantar kimanin watanni shida da suka gabata. Gwamnati ta kashe makuden kudade amma abin bakin ciki, an kona makarantar kurmus.
"Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna akwai zagon kasa domin ban ga dalilin da zai sa makaranta irin wannan, wacce ba a riga an hada ta da wutar lantarki na kasa ba, babu lantarki, babu injin janareta, amma kawai sai ka ga wuta a hawa na karshe a makarantar."
Shugaban makarantar, Saidu Umaru, ya ce ajujuwa 19 ne da dakin gwaje-gwaje uku suka kone sakamakon gobarar da ta faru a safiyar ranar Litinin kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng