Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

Jagoran darikar Tijjaniya a Aljeriya, Sheikh Aliyu Bil Arabi, Sheikh Tahir Usman Bauchi da sauran manyan malamai sun taru a birnin Kano don gudanar da addu'ar zaman lafiya.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya karbi bakuncinsu ya halarci taron addu'ar dake gudana a filin kwallon Sani Abacha dake unguwar Kofar Mata, Kano.

Shugaba Muhammadu Buhari ya samu wakilcin karamin Ministan noma, Mustapha Baba Shehuri.

Babban hadimin Gwamnan Kano kan sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin wannan addu'a.

Yace daga cikin mahalarta akwai mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya wakilci Gwamnansa, Muhammadu Badaru Abubakar.

Kalli hotuna:

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari, Gwamnoni, Ministoci sun yi ta'aziyyar Sheikh Ahmad Bamba

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, manyan Maluma sun taru da Kano don addu'a
Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, manyan Maluma sun taru da Kano don addu'a Hoto: SSA Social Media, Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Kalli bidiyo:

Asali: Legit.ng

Online view pixel