Sarkin Kano, Manyan Malamai, daruruwan mutane sun halarci Jana'izar Sheikh Ahmad Bamba

  • Daruruwan mutane sun halarci Sallar Jana'iza tare da birne babban malamin addini, Sheikh Ahmad BUK
  • Jana'izar ta gudana ne a masallacin Darul Hadith bayan Sallar Juma'a a jihar Kano
  • An birneshi a makabartan Dandolo, Goron Dutse

Kano - An yi Sallar Jana'iza tare bizne babban malamin hadisi, Sheikh Dr Ahmad Muhammad, wanda aka fi sani da 'Kala Haddasana' wanda ya rasu da safiyar Juma'a.

An birne Malamin ne a makabartar Dandolo dake Goron Dutse, jihar Kano bayan Sallar Juma'a.

Manyan Malamai, yan siyasa, daliban ilmi, yan'uwa, abokan arziki, da daruruwan mutan gari sun hallarci jana'izar Malamin.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wanda yayi takakkiya kansa.

Sarkin Kano, Manyan Malami, daruruwan mutane sun halarci Jana'izar Sheikh Ahmad Bamba

Asali: Facebook

Kalli bidiyon Jana'izar:

Asali: Legit.ng

Online view pixel