Da duminsa: An yi garkuwa da tsohon Shugaban NPA a jihar Kano

Da duminsa: An yi garkuwa da tsohon Shugaban NPA a jihar Kano

Sumaila - Yan bingida sun yi awon gaba da tsohon Manaja Janar na hukumar tashoshin jirgin ruwa (NPA), Bashir M Abdullahi, a jihar Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da Bashir Abdullahi a gonarsa dake kauyen Gomo, karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano.

Wannan abu ya auku ne ranar Laraba.

Wani mazaunin garin Gomo ya bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne lokacin da yaje kallon yadda abubuwa ke gudana.

Kakakin hukumar yan sanda bai tabbatar da labarin ba.

Da duminsa: An yi garkuwa da tsohon Shugaban NPA a jihar Kano
Da duminsa: An yi garkuwa da tsohon Shugaban NPA a jihar Kano
Source: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Source: Legit.ng

Online view pixel