Kwana 2 bayan kaddamar da e-Naira, masu Andriod na kuka yayinda manhajar ta samu matsala a Google Store

Kwana 2 bayan kaddamar da e-Naira, masu Andriod na kuka yayinda manhajar ta samu matsala a Google Store

  • Bayan mutane 100,000 sun saukar da manhajar kan wayoyinsu ta Andriod, manhajar ta yi batan dabo daga Google Play Store
  • Amma ga masu amfani da wayoyin iPhone, har yanzu manhajar na nan kuma zasu iya saukarwa
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudin intanet din ne ranar Litinin gabanin tafiyarsa Saudiyya

Manhajar eNaira ya yi batan dabo daga kan Google Play Store kimanin kwanaki biyu bayan kaddamar da ita, rahoton Punch ya nuna haka.

Wannan ya faru ne bayan sama da mutum 100,000 masu amfani da waya kalar Android sun saukar da manhajar don amfani.

Amma ga masu wayar iPhone, manhajar har yanzu tana nan kuma ana cigaba da amfani da ita.

Binciken da Legit ta gudanar ya tabbatar da cewa lallai manhajar ta bace a Google Play Store yau Laraba.

Kara karanta wannan

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

Domin amfani da kudin yanar gizo na eNaira, ana bukatar mutum ya saukar da manhajar domin amfani cikin sauki.

Kwana 2 bayan kaddamar da e-Naira, masu Andriod na kuka yayinda manhajar ta samu matsala a Google Store
Kwana 2 bayan kaddamar da e-Naira, masu Andriod na kuka yayinda manhajar ta samu matsala a Google Store
Asali: Getty Images

Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudin intanet na Najeriya, e-Naira, ranar Litinin, 25 ga Oktoba, a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.

Wadanda ke hallare a taron kaddamar da kudin sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da kudin intanet na Najeriya

CBDC wakilci ne na tsarin kudaden intanet masu cikakken iko da ake samar da su kamar yadda Babban Banki ke samar da kudi gama-gari.

Alhakin kai tsaye ne na Babban Banki ke samar dashi. Ba ana nufin maye gurbin tsabar kudi da tsarin ajiyar banki bane, ana nufin su yi aiki kunnen doki a matsayin karin nau'in hanyar biyan kudi da karba.

Kara karanta wannan

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

Ta yaya CBDC zai gudana?

CBN ya yi bayanin cewa tsarin eNaira CBDC ya hada da matakai 4 zuwa cikakken aiwatarwa da kuma tafiyarwa.

CBN ne ke da alhakin kerawa, kirkira da adana CBDC.

Za a rarraba CBDC ga cibiyoyin kudi da masu hada-hadar kudi masu lasisi wadanda za su ba da su ga mutane da sauran kasuwanni.

Cinikayya da CBDC na iya kasancewa akan yanar gizo ko akasin haka. Mutane da kamfanoni za su iya huldar kasuwa dashi nan take ta hanyar tashoshin biyan kudi na yanzu da na nan gaba (misali wayar hannu).

CBN za ta ci gaba da sa ido da kula da CBDC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel