Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar

Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar

  • Yan ta'addan Boko Haram sun tashi gari a jihar Yobe ranar Asabar
  • Masu shaidar ganin ido sun ce yan ta'addan sun shiga garin cikin moto akalla 10
  • Arewa maso gabashin Najeriya na cigaba da fuskantar matsalar tsaro

Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne cikin motoci kimanin goma sun dira garin Katarko, dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe ranar Asabar, 23 ga Oktoba 2021.

DailyPost ta ruwaito cewa majiyoyi sun bayyana yadda yan ta'addan gungun suka shiga cikin garin misalin karfe takwas na safe suna harbin kan mai uwa da wabi.

Majiyar ta kara da cewa jami'an Sojojin dake wajen sun yi artabu da su.

A cewarsa majiyar:

"Sai da muka arce don kare rayukanmu."

Read also

Muna neman gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Sokoto, Tambuwal

Garin Katarko na da nisan Kilomita 20 da Damaturu, birnin jihar kuma sun dade suna fuskantar hare-hare daga wajen Boko Haram.

Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar
Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar Hoto: AlJazeera
Source: UGC

Source: Legit

Online view pixel