Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi

Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi

Jihar Kano - Kungiyar masu shayi a jihar Kano sun yanke shawarar kara farashin shayi maras madara wanda aka fi sani da 'Empty' daga N30 zuwa N50.

Wannan sabon kari ai fara aiki ne daga ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021.

Kakakin kungiyar masu shayin, Rayyanu Jibril, ya bayyanawa BBC Hausa cewa sun yi wannan kari ne saboda tsadar sikari da gawayi.

A cewarsa:

"Buhun Sukari yanzu ya koma N21,000 daga N13,000 kuma gawayi ya tashi N2500 daga N1500."

Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi
Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi Hoto: BBC Hausa
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Source: Legit

Tags:
Online view pixel