Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

  • Jami'an hukumar tsaro na farin kaya, DSS, sun sake tasa keyar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu zuwa ma'adanarsu
  • Hakan ya biyo bayan dage shari'ar da aka yi zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba bayan ya musanta sabbin zargin da FG ke masa
  • Gwamnatin tarayya ta sabunta zargin da ta ke wa Kanu inda ta kara da zargin cin amanar kasa da ta'addanci

FCT, Abuja - Jami'an tsaron farin kaya, DSS su sake iza keyar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB zuwa ma'adanarsu.

An gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargi bakwai da gwamnatin tarayya ke masa a ranar Alhamis, Daily Trust at ruwaito.

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa
Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa. Hoto daga thenationonlinenet.ng
Asali: UGC

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Kanu ya musanta zargin da ake masa da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

Tawagar lauyoyin Kanu da suka samu jagorancin Ifeanyi Ejiofor, sun kalubalaci tsaresa a hannun hukumar DSS tare da bukatar a mayar da shi gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Sai dai, Mai Shari'a Binta Nyako ta babban kotun tarayyan ta yi fatali da wannan bukatar.

Daga nan ta dage shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba kuma aka fitar da shugaban IPOB din a wata farar Hilux.

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

A wani labari na daban, wakilin Birtaniya a Najeriya ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja domin sauraron shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

TheCable ta ruwaito cewa, wakilin Ingilan ya isa farfajiyar kotun a wata mota fara kirar Toyota Highlander wurin karfe takwas da minti uku na safiyar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yadda mawallafin ShaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

Kanu wanda ke da shaidar zama dan kasar Birtaniya, ya shiga hannun hukuma a Najeriya ne a watan Yuni kuma an dawo da shi gida Najeriya domin a gurfanar da shi kan zargin cin amanar kasa da ake masa.

Ya tsere Ingila a shekarar 2017 bayan ya tsallake belin da aka bada shi, TheCable ta wallafa.

Tariq Ahmad, karamin ministan harkokin waje na Birtaniya, ya ce Ingila ta na bukatar bayanin Najeriya kan yadda ta cafke Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel