Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

  • Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa yan fashin daji sun fara sako mutanen da suka kama saboda babu abincin ba su
  • Dakta Abdullahi Shinkafi, mataimakin kwamitin tsaro, yace matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka suna haifar da ɗa mai ido
  • Yace rashin sadarwa ta sa maharan na tura sako ta wasika, kuma jami'an tsaro na amfani da wannan damar wajen damke su

Zamfara - Mataimakin shugaban kwamitin nemo hanyoyin daƙile ayyukan yan bindiga a Zamfara, Dakta Abdullahi Shinkafi, yace yan fashin daji sun rasa abincin da zasu ciyar da mutanen da suka kama.

Channels tv ta ruwaito Shinkafi na cewa matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka sun saka yan ta'addan sako mutane ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Shinkafi ya yi wannan furucin ne yayin wata fira a Gusau, lokacin da yake yaba wa matakan daƙile yawaitar ayyukan ta'addanci a jihar.

Dakta Abdullahi Shinkafi
Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shinkafi yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Akwai wasu mutum 11 da mahara suka sace, sun sako ɗaya domin ya sanar da cewa sai an biya N200,000 a kan kowannen su."
"Kafin tattaunawa ta yi nisa yan fashin suka nemi a biya miliyan N20,000 kan kowane mutun ɗaya. Iyalan mutanen suka ƙi tura kuɗin, dole ta sa suka sako mutanen kyauta."
"A cewarsu babu abincin da zasu cigaba da ciyar da su. Saboda haka matakan suna haifar da ɗa mai ido."

Shin datse hanyoyin sadarwa yana taimakawa?

Shinkafi ya kara da cewa game da datse hanyoyin sadarwa, yan fashin dajin sun tura saƙon wasika zuwa ga mutanen Shinkafi da kuma sarkin Zurmi.

Ya bayyana cewa yan bindigan sun yi amfani da takardar shedar siyan babur wajen rubuta wasiƙa ga mutane domin neman kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Ya kuma tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi amfani da adireshin kamfani. mashin ɗin, wajen gano yan ta'addan kuma aka damƙe su.

A wani labarin kuma Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina

Shugaban hukumar, Wada Chedi, yace da farko sun fara samun bayanan sirri amma daga bisani suka bi diddigin lamarin har suka tabbatar.

A cewarsa yan sumoga na ƙara wa tankin mai girma sannan su cikashi a gidan mai sukai wa yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel