Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

  • Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da take takkinsa tare da hana shi sakat a rayuwarsa
  • Ya bayyana bukatar gwamnati ta saki fasfo dinsa, tare da barinsa ya tafi kasar waje nemo magani
  • Ya kuma maka gwamnati a kotu, inda ya nemi gwamnati ta biya shi diyyar makudan kudade

Abuja - Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya zargi Gwamnatin Tarayya da yi masa alama tare da matarsa, Zeenat, saboda rike fasfo dinsu watanni uku bayan an sallami ma’auratan tare da wanke su daga manyan laifuka a babbar kotun jihar Kaduna.

Ma'auratan, an hana su samun sabbin fasfo na kasa da kasa domin su yi balaguro zuwa kasashen waje don neman lafiya bayan da aka ruwaito jami'an tsaro sun rasa takardun a cikin shekaru shida da suke tsare.

Kara karanta wannan

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat
Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa a harabar kotu | Hoto: mrf.io
Asali: UGC

Sheikh El-Zakzaky, wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi 17 ga watan Oktoba a wata hira da gidan talabijin na Press TV a Abuja, ya kuma zargi gwamnati da kin bayyana wani dalili na yin hakan, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, ba su da niyyar tserewa daga kasar tun lokacin da Kotu ta bayyana cewa ba su da laifi daga tuhume-tuhume takwas da ake yi musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake bayyana halin da ya shiga yayin da yake tsare tare da matarsa, Malam Zakzaky ya bayyana cewa, har yanzu akwai sauran alburusai a jikinsa da na matarsa wanda ba a cire ba.

Zakzaky ya maka gwamnatin Buhari a kotu

Duba da rashin lafiyarsu da kuma hana su fita domin a kula dasu a kasar waje, Malam Zakzaky ya shigar da kara kotu kan gwamnatin tarayya, hukumar DSS da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Ya bukaci gwamnati ta biya shi tare da matarsa diyyar kudade da suka kai N2bn kowannensu.

Wannan na fitowa ne cikin wata takardar kara da SaharaReporters ta ruwaito daga lauyan Zakzaky, Femi Falana (SAN).

Karar ta bayyana zarge-zarge daban-daban da Zakzaky ke yi kan gwamnati da hukumominta na take hakkinsa na hanashi ketare kasa.

Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel