Sarkin Gargajiya ya sayar da Taransfoma 2 da aka bawa kauyensa, an damkesa tare da mutum 2

Sarkin Gargajiya ya sayar da Taransfoma 2 da aka bawa kauyensa, an damkesa tare da mutum 2

  • An damke basarake da laifin cutar al'ummarsa a jihar Akwa Ibom
  • Jami'an yan sanda sun gurfanar da shi tare da wasu mutum biyu
  • Ya sayar da Taransfoman samawa garinsa wutan lantarki guda biyu

Uyo - Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom sun damke wani Sarkin Gargajiya da wasu mutum biyu kan laifin sayar da taransfoma biyu masu nauyi 500KVA da aka bayar da samar da lantarki.

Kakakin hukumar na jihar, SP Odiko MacDon, ya bayyana hakan ga manema labarai a Uyo ranar Juma'a, rahoton Premium Times.

Ya bayyana sunan mai sarautan, Aniefiok Udo, Dagacin Nsiak a karamar hukumar Ikot Ekpene.

Hukumar cigaban yankin Neja Delta NDDC ce ta baiwa kauyen Nsiak wadannan Taransfomomi biyu kyauta.

Kara karanta wannan

Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko

Sarkin Gargajiya ya sayar da Taransfoma 2 da aka bawa kauyensa, an damke tare da mutum 2
Sarkin Gargajiya ya sayar da Taransfoma 2 da aka bawa kauyensa, an damke tare da mutum 2
Asali: Twitter

Ya ce Dagacin tare da abokan laifinsa sun amsa laifin kuma hakan ya taimaka wajen gano Taransfomomin.

SP Odiko yace abokan laifin sune Eteobong Udo da Uduak George.

Yace:

"A ranar 23 ga Satumba, 2021, sashen yaki da yan daba dun damke dagacin kauyen Nsiak a kramar hukumar Ikot Ekpene, Aniefiok Mfon, Eteobong Udo da Uduak George."
"Bincike ya nuna cewa wadannan mutane sun hada baki wajen sayar da Taransfomomi 500KVA biyu da hukumar Neja Delta ta baiwa kauyen."

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

A bangare guda, akalla rayuka 12 aka kashe yayin farmakin da 'yan bindigan daji suka kai kauyen Sakajiki da ke masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Bayan kimanin shekaru 2, za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a.

Ya ce an samu wadanda suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin kuma ba don taimakon jami'an tsaro ba, da abun ya fi haka muni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel