El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

  • Shekaru bayan kafa dokar tantance wa'azi, gwamnan Kaduna ya kafa majalisa ta musamman
  • Daga cikin mambobin majalisar akwai Madaki Zazzau, Alhaji Munir Jafaru
  • El-Rufa'i yace an kafa kwamitin ne don tabbatar da Malamai ba sa wa'azin haddada rigima tsakanin jama'a

Kaduna - Gwamnan Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya kafa majalisar tantance Malamai masu wa'azin addini a fadin jiharsa don tabbatar da cewa wanda ya cancanta kadai za'a bari yayi wa'azi.

A taron rantsar da mambobin majalisar da akayi ranar Juma'a, 15 ga Oktoba 2021 da ya gudana a gidan Sir Kashim Ibrahim, El-Rufa'i yace addini alaka ne tsakanin mutum da ubangijinsa, ba abin amfani wajen neman matsayin siyasa ko kudi ba.

Hakazalika yace addini ba abinda za'a rika amfani da shi wajen lalata dukiyan juna da kashe-kashe rayuka bane.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 7 da ke rike da tarin albashin malaman makarantun Firamare

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a jawabinda ya saki ranar Asabar kuma Legit ta samu.

A cewarsa:

"Yawancin al'ummar jihar Kaduna masu bin addini ne sosai, kamar sauran yan Najeriya. Amma jihar Kaduna na daga cikin jihohin aka dade ana rikicin addini."
"Yanu muna da dokar yin wa'azi kuma mun lashi takobin kawo karshen bata gari masu bata addini. Addini alakar mutum ne da ubangijinsa, na abinda cinikin kudi ko mukamin siyasa ba."
"Hakazalika ba abin rikici, kisan kai, lalatan dukiar al'umma da fadace-fadace tsakanin mabanbanta addini bane."

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna
El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Wani aiki majalisar a zata yi?

Yayin jawabi da mambobin majalisar da ya ranstar, El-Rufa'i yace suna da hakkin tabbatar da cewa Malaman addini basu haddasa rikici tsakanin jama'a.

A cewarsa, mambobin kwamitin su tantance masu wa'azi don tabbatar da ko mutum ya cancanta yayi.

Kara karanta wannan

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

Yace:

"Mambobin majalsar tantance wa'azi na da aiki mai muhimmanci na tabbatar da cewa Malaman adidni basu gwara kan jama'a ba da kuma tabbatar da cewa masu bauta basu takurawa wasu."
"Ina tabbatar muku da cewa gwamnatin Kaduna zata taimaka muku wajen yin aikinku don tabbatar da cewa wadanda suke da ilimi da horo suna wa'azi ba tare da haddasa rikici cikin al'umma ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel