Hare-haren ta’addanci: Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta akan zuwa wadannan jihohi 12 na Najeriya

Hare-haren ta’addanci: Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta akan zuwa wadannan jihohi 12 na Najeriya

Kasar Burtaniya ta ba ‘yan kasarta da ke ziyartan Najeriya shawarwari na tafiye-tafiye. Ta ambaci wasu jihohi 12 a kasar ta Afrika ta yamma da za su gujewa.

Shawarar da Burtaniya ta bayar ta Ofishinta na FCO na zuwa ne a yayin da ake tsaka da yiwuwar 'yan ta'adda su kai hare-hare a Najeriya da kuma tarurruka don bikin cika shekara daya da zanga-zangar #EndSARS.

Hare-haren ta’addanci: Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta akan zuwa wadannan jihohi 12 na Najeriya
Hare-haren ta’addanci: Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta akan zuwa wadannan jihohi 12 na Najeriya Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP
Asali: Getty Images

A wani jawabi da aka wallafa a shafinta, ta nuna damuwa kan zanga-zanga da tsauraran matakan tsaro a manyan biranen saboda shari’ar jagoran masu fafutukar yankin Biyafara, Nnamdi Kanu.

Gwamnatin kasar wajen ta kuma bukaci ‘yan kasarta da su dunga bibiyar kafofin watsa labarai na gida, da kuma gujema kowani irin zanga-zanga ko manyan taruka.

Kara karanta wannan

A karshe PDP ta bukaci Kotu ta tsige Gwamnan Zamfara da duk wadanda suka koma APC

Burtaniya ta lissafa jihohin na Najeriya kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Jihar Borno

2. Jihar Yobe

3. Jihar Adamawa

4. Jihar Gombe

5. Jihar Kaduna

6. Jihar Katsina

7. Jihar Zamfara

Yankunan ruwa

8. Jihar Delta

9. Jihar Bayelsa

10. Jihar Ribas

11. Jihar Akwa Ibom

12. Jihar Cross River

Hukumar ta FCDO ta ba da shawara game da tafiye-tafiye ban da muhimmai zuwa:

1. Jihar Bauchi

2. Jihar Kano

3. Jihar Jigawa

4. Jihar Neja 5.

Jihar Sokoto

6. Jihar Kogi

7. Tsakanin kilomita 20 daga kan iyaka da Nijar a jihar Kebbi

8. Jihar Abia

9. Yankunan da ba su da kogi na jihohin Delta, Bayelsa da Ribas

Kara karanta wannan

Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa

Babban Hafsan tsaron Najeriya ya tabbatar da kisan Shugaban ISWAP, Mus'ab Albarnawy

A wani labarin, babban Hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da kisan shugaban kungiyar yan ta'addan daular Islamiyya a yammacin Afrika ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda hira da manema labarai da fadar shugaban kasa ta shirya a AsoVilla, Abuja, DailyTrust ta ruwaito.

Irabor yace:

"Ina mai tabbatar muku cewa Abu Mus'ab ya mutu. Ya mutu kuma ba zai taba tashi ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel