Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

  • Mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa na harkokin man fetur, Sanata Ifeanyi Ubah ya yi kira akan sakin Nnamdi Kanu
  • A cewar Sanatan, sakin Kanu zai kawo karshen tashin-hankali da rikicin da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya
  • Kamar yadda ya bayyana, akwai manyan ‘yan siyasan da su ke amfani da damar tsare Kanu da gwamnati ta yi wurin tada tarzoma

Legas - Mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa na man fetur, Sanata Ifeanyi Ubah ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan sakin Nnamdi Kanu.

Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, sanatan mai wakiltar mazabar Anambra ta kudu ya bukaci a saki shugaban IPOB din.

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanatan Nigeria
Shugaban haramtaciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Photo credit: Marco Longari/AFP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ubah wanda yanzu haka yake neman takarar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar YPP a zabe mai zuwa ya ce akwai ‘yan siyasan da su ke amfani da damar tsare Kanu wurin tayar da tarzoma a yankin.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Kamar yadda Ubah ya bayyana, sakin Mazi Nnamdi Kanu cikin gaggawa zai kawo garanbawul ga matsalolin tsaron kuduncin Najeriya.

A cewar sa ya kamata gwamnati ta duba lamarin

Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta natsu kuma ta kalli lamarin da idon basira, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne yayin wani taro da ya yi da ‘yan kasuwan Anambra a kasuwar duniya ta Alaba da ke jihar Legas.

Kamar yadda ya ce:

Akwai shugabannin matasa da su ka yi amfani da damar tsare Kanu wurin kai wa sanatan ziyara inda su ke bukatar ya sa baki akan batun tsare Mazi Nnamdi Kanu kuma sun bukaci ya duba lamarin.

A bangaren sanatan ya ce akwai kokarin da ake ta yi ta karkashin kasa don ganin an yi abinda ya dace akan lamarin, ya kuma yi alkawarin isar da sakon su ga gwamnatin tarayya.

Anan ne sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta taimaka don kawo mafita dangane da lamarin. Kamar yadda ya bayyyana:

“Mun yarda da cewa matsalolin rashin tsaron da ke Anambra za su kare saboda yadda ‘yan siyasa su ke daukar nauyin ‘yan bindiga su na fakewa da wasu dalilai, idan aka sake shi ba su da wani uzuri da za su fake da shi.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel