Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

  • Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Honarabul Sha'aban Sharada, ya ce idan aka yi zabe a yanzu a Kano, warwas za a yi wa APC
  • Kamar yadda dan majalisar ya bayyana, sun yi taro a gidan Sanata Shekarau ne domin kai wa jam'iyyar daukin gaggawa a kan lokaci
  • A cewarsa, a halin yanzu, 'yan majalisa da wasu jami'an gwamnati suna zunden gwamnatin kan kwabar da ta ke yi a jam'iyyar

Kano - Honarabul Sha'aban Sharada, dan majalisar wakilai kuma mamban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga Kano, ya ce jam'iyyarsu ba za ta iya cin zaben gwamnoni ba a Kano a halin da ake cikin.

Dan majalisan ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi da BBC kan rikicin da ya sarke jam'iyyar a Kano.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Hon Sha'aban: Da za a sake zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC
Hon Sha'aban: Da za a sake zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce rikicin da ake ciki ne yasa suka yi wani taron masu ruwa da tsaki a gidan Sanata Ibrahim Shekarau a ranar Talata.

Bayan taron, 'yan majalisar sun rubuta korafi tare da mika shi ga shugaban jam'iyyar na rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni.

A tattaunawar, Sha'aban ya ce daukin da suka kai wa jam'iyyar ya yi daidai a wannan lokacin.

"Mun tattauna kan maganganu masu muhimmanci 3. Mun yi fatali da zabukan shugabancin jam'iyya na gundumomi da kananan hukumomi wanda gwamnatin jihar ta yi kuma ba mu goyi bayan lamarin kwata-kwata."
“Saboda an bai wa wadanda basu dace ba kambun jam'iyyar domin su mulki jama'a a matakin gunduma da kananan hukumomi.
“Da yawa daga cikin 'yan majalisar jiha da wasu jami'an gwamnati suna ta zinden gwamnatin jiha. Abu daya muke so, muna son komai ya koma daidai tun kafin lokaci ya kwace mana", Sharada yace

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

"Da a ce rudu muke son kawowa, wadannan jajirtattaun mambobin da sun goyi bayan abinda Ganduje ya ke kuma su yi tsit har sai an fara kamfen, kamar dai yadda wasu daga cikinmu suka yi," yace.
Ya kara da cewa, "Idan a yau aka yi zaben gwamnoni a Kano, babu shakka jam'iyyar mu faduwa za ta yi. Ba za mu so a ci galaba kan jam'iyyarmu ba, hakan yasa muka kawo dauki."

Kamar yadda yace, Mai Mala Buni ya tabbatar da cewa ya ji kokensu.

Amma kuma ya ce duk abubuwan da ke faruwa, shugaban rikon kwaryan jam'iyyar bai san da su ba.

"Na yadda cewa mutum ne mai adalci wanda ba shi da tsoro kuma zai yi abinda ya dace," ya kara da cewa.

Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, cikin mutane ya caccaki Abdullahi Ganduje, bayan gwamnan jihar Kanon ya nuna kamar bai san da shi a wurin wani taro ba.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali

Kamar yadda jaridar ThisDay ta wallafa, taron kaddamar da wani littafi ne wanda fitaccen dan jarida Dr. Amanze Obi ya rubuta, kuma Ihedioha da Ganduje duk sun halarta.

Lamarin ya fara ne lokacin da gwamnan jihar Kano, wanda shi ne babban bako na musamman a wurin kaddamar da littafin ya gaida dukkan jiga-jigan da ke teburi na musamman, amma bai ko duba inda Ihedioha ya ke ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel