Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd

Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd

  • Bidiyoyin shagulgula tare da bidirin bikin kamun Furodusa Abba Maishadda tare da masoyiyarsa Hassana Muhammad sun fara bayyana
  • Bikin kamun ya samu halartar jaruman masana'antar har da fitattun mawaka irinsu Ado Gwanja wadanda suka nishadantar da jama'a
  • Za a daura auren masoyan ne a ranar 13 ga watan Maris wanda yayi daidai da ranar Lahadi a garin Gombe da ke arewa maso gabas a Najeriya

Shagalin bikin Furodusa Abubakar Maishadda da jaruma Hassana Muhammad ya kankama inda aka yi bikin kamunsu a ranar Juma'a.

Babu shakka biki ya yi biki tunda an ga jarumai mata da maza, mawaka da jiga-jigai daga masana'antar Kannywood sun hallara.

Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd
Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd. Hoto daga @adogwanja
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Daga cikin bidiyoyin da Legit.ng ta samo, an ga mawaki Ado Gwanja yana wake ango inda yake ta masa barin dukiya yayin daga bisani mawakin ya koma wakarsa a filin bikin.

Ga wasu daga cikin bidiyoyin a kasa ku sha kallo:

Kamar yadda katin gayyatar bikin ya nuna, za a daura auren masoyan ne a ranar 13 ga watan Maris a garin Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel