Gwamnan Najeriya Mai Karfin Iko Ya Samu Mukami A Morocco, Wata Daya Kafin Wa'adin Ya Kare

Gwamnan Najeriya Mai Karfin Iko Ya Samu Mukami A Morocco, Wata Daya Kafin Wa'adin Ya Kare

  • Gwamna Fayemi Kayode na Jihar Ekiti ya samu mukami na shugabancin kungiyar yankunan nahiyar Afirka, FORAF, bayan kada kuri'a da aka yi a Morocco
  • Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Najeriyan ya samu wannan babban mukamin ne kimanin wata daya kafin karewar wa'adinsa
  • Kasashen da suka hallarci taron sun hada da Kenya, Najeriya, Afirka ta Kudu, Burkisa Faso, Kamaru, Cote d'Ivoire, Madagascar, Mali, Jamhuriyar Nijar dss

Morocco - An nada shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, kuma gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Femi mukamin shugaban kungiyar yankunan Afirka, FORAF.

A cewar sakon kar ta kwana da direktan watsa labarai na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya tura, an zabi Gwamna Kayode matsayin shugaban Kungiyar Yankunan Afirka a Saidia a zaben da aka yi da safe a birnin Saidia a Oujda na Casablanca a Morocco, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hotuna sun ba da mamaki yayin da Sarkin Musulmi ya gana da wani gwamnan Kudu

Gwamna Kayode Fayemi.
Gwamnan Najeriya Mai Karfin Iko Ya Samu Mukami A Morocco, Wata Daya Kafin Wa'adin Ya Kare. Hoto: Kayode Fayemi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za a iya tunawa, an fara taron na FORAF ne daga ranar 8 zuwa 10 na watan Satumban 2022, karo na farki a Saidai (Morocco), karkashin jagorancin Mai Martaba Sarki Mohammed VI.

United Cities and Local Governnment of Africa, UCLG Africa tare da hadin gwiwar Kungiyar Association of Moroccan Regions, ARM, da Directorate of Territorial Collectivities, DGCT, na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida na Masarautar Morocco suka hada taron.

An yi taron ne don aiwatar da shawarwarin da aka cimma a babban taron UCLG Africa karo na 8 da aka yi a Marrakech a watan Nuwamban 2018, a cewar Mrs Fatimetou Abdel Malick, shugaban UCLG Africa.

Kasashen da suka hallarci taron sun hada da Najeriya, Afirka ta Kudu, Burkisa Faso, Kamaru, Cote d'Ivoire, Kenya, Madagascar, Mali, Jamhuriyar Nijar da sauransu.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi

Kimanin mutane fiye da 400 ne suka halarci taron.

Gwamna Fayemi ya sallami baki ɗaya hadimansa daga bakin aiki

A wani rahoton, Kayode Fayemi, ya sallami dukkan hadimansa na siyasa da ya naɗa a gwamnatinsa yayin da lokacin miƙa mulki ke kusantowa.

A cewar wata sanarwa da Daily Trust ta tattaro, gwamnan ya ɗauki matakin ne domin biyayya ga dokokin miƙa mulki na jiha da kuma tabbatar da an biya kowane mai rike da Ofis haƙƙinsa da alawus ɗin zango.

Sanarwar na ɗauke na sa hannun Sakataren gwamnatin jihar, Foluso Daramola, kuma an raba wa manema labarai kwafinta a Ado-Ekiti, babban birnin jihar a ƙarshen makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164