Da Duminsa: An Yi Wa Tsohon Gwamnan Najeriya Tiyata A Baya, Hotuna Da Bidiyo Sun Fito

Da Duminsa: An Yi Wa Tsohon Gwamnan Najeriya Tiyata A Baya, Hotuna Da Bidiyo Sun Fito

  • An yi wa tsohon gwamna a Najeriya, Ayodele Fayose tiyata a bayansa a wani asibiti a kasar waje
  • An yi masa tiyatan cikin nasara bayan tsohon gwamnan na Jihar Ekiti ya samu rauni a yayin zaben gwamna na jiharsa a 2018
  • Hadimin Fayose a bangaren watsa labarai, Lere Olayinka, ya ce an yi wa mai gidansa tiyata sai biyu cikin watanni shida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An yi wa tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose tiyata a bayansa a wani asibit a kasar waje.

An ga tsohon gwamnan na Jihar Ekiti, wanda ya sha kaye hannun wanda ya gaje shi, Kayode Fayemi, a bidiyo tare da likitoci da malaman jinya suna kula da shi a asibiti.

A cewar dan uwansa, Isaac da kuma tsohon hadiminsa, Lere Olayinka, wannan shine karo na biyu da aka yi wa tsohon gwamnan tiyata a cikin watanni biyar.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Ayo Fayose
Bidiyo Da Hotunan Fayose Yayin Da Aka Masa Tiyata a Kasar Waje. Hoto: Lere Olayinka.
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A faifan bidiyon, an ga Fayose, wanda jigo ne a jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ana taimaka masa ya zauna.

An tattaro cewa tsohon gwamnan na Ekiti ya samu rauni a bayansa a 2018 hakan ya sa aka yi masa tiyatan.

Ga hotuna da bidiyon Fayose a asibitin.

Da ya ke martani kan lamarin, mataimaki na musamman kan bangaren sabuwar kafar watsa labarai na Fayose, Lere Olayinka, ya taya mai gidansa murna bisa yin tiyatar cikin nasara.

Olayinka ya ce:

"Fayose ya yi tiyata sai biyu cikin watanni biyar. Manyan tiyata biyu cikin watanni biyar.
"Guda daya a watan Fabrairu a wutansa yanzu kuma wani guda daya a baya. Sakamakon harin da aka kai masa yayin zaben gwamnan Ekiti a 2018. Wannan ikon Allah ne. Ina maka fatan samun sauki cikin gaggawa Osokomole."

Kara karanta wannan

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

Atiku ya shiga tsaka mai-wuya a 2023, Fayose ya ce har abada Wike ba zai goyi bayansa ba

A wani rahoton, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Peter Fayose, ya yi bayanin abin da ya sa Nyesom Wike ba zai taba goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 ba.

A wata hira da Premium Times ta yi da Ayo Peter Fayose, ya fadi dalilin Gwamna Nyesom Wike na juya baya ga ‘dan takaran na PDP a zaben shugaban kasa.

Fayose ya kara nanata matsayarsa na cewa bayan Muhammadu Buhari ya kammala shekara takwas, abin da ya kamata shi ne shugabanci ya koma kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164