Siyasa

Sanotoci sun ki amincewa da wanda Shugaban kasa ya zaba a kujerar PENCOM
Wanda Buhari ya zaba ta zama Shugabar PENCOM ta gaza samun cikakkiyar karbuwa a Majalisar tarayya. Wasu a Majalisar sun yi kememe, sun hau kujerar na-ki a kanta
Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna
Mawakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zama dan siyasa, Malam Ibrahim Sale Yala, ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba kakakin majalisar Kaduna shawara.
Dalilanmu na jingine yajin aiki - Kungiyar Kwadago ta magantu
Takardar na dauke da sa hannun shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba, shugaban TUC, Quadri Olaleye, sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, sakataren TUC, Musa Lawal Ozigi
Jihohin Neja-Delta 2 sun cigaba da rigima kan rabon rijiyoyin danyen mai
Nyesom Wike ya maidawa Diri martani na cewa hukumar RMFAC ta daina biyan jihar Ribas kason kudin mai. Nyesom Wike da kuma Douye Diri duk ‘Yan jam’iyyar PDP ne.
Sabbin alkalan kotun koli: Buhari ya aikawa majalisa sunayen mutanen 8
Sunayen mutanen da Buhari ya aika sun hada da; Lawal Garba (arewa maso yamma), Helen Ogunwumiju (kudu maso yamma), Abdu Aboki (arewa maso yamma) da M M Saulawa
Yajin aiki: Yadda Kungiyoyin TUC da NLC su ka yaudari mutane – Cibiya
Cibiyar CHRICED ta yi Allah-wadai da janye yajin-aikin da aka yi jiya. Dr. Ibrahim Zikirullahi ya ce ‘Yan kwadago sun dade su na yaudarar al’umma tun 1999.
ASCAB ta bankado tiriliyan N94.3 da aka karkatar, ta rubutawa Buhari wasika
Wata babbar kungiyar hadaka ta kungiyoyi da ke rajin tabbatar da daidaituwar al'amura bayan annobar korona (ASCAB) ta bayyana cewa ta bankado tiriliyan N94.3 da
Da duminsa: Buhari ya kaddamar da wani babban aiki da aka saka sunan Jonathan (Bidiyo)
An yi bikin ne a tashan jirgin kasa na Agbo inda aka saka wa tashar sunan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan don karrama shi saboda gudunmuwarsa.
Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas
Bayan hutun shekara da ta tafi na tsawon fiye da watanni biyu, Majalisar dattawan Najeriya ta dawo zama a yau Talata, za ta tattauna muhimman batutuwa da dama.
Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani
Tolu Ogunlesi, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna da ya fara yajin aikinsa, The Cable.
Tun farkon mulkin Buhari, ba a fara da sa'a ba - Oyegun ya bayyana manyan kalubalen APC
John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa'a tun farkon shi. The Cable ta wallafa haka.
Sarautar Zazzau: Babban Malamin addini, Gumi ya bada wata mafita 1 a sauki
Mun ji cewa Malamin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud ya shawarci Hukuma game da yadda ake zaben Shugaba. Gumi ya ce al’ummar Musulmai na bukatar hadin kai.
Ka nuna aiki ɗaya da ka yi wa Rivers: Gwamna ya kalubalanci Ministan Buhari
Gwamna Nyesome Wike na jihar Ribas, ya kalubalanci ministan sufuri Rotimi Amaechi da ya nuna aiki guda daya da ya yiwa jihar, cewa idan ya nuna shi zai sauka.
Gwamnatin Buhari za ta fara rabon kudi a Mahaifar Goodluck Jonathan
A makon jiya Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin CCT a Jihar Bayelsa a kokarin Muhammadu Buhari na fito da mutane miliyan 100 daga cikin talauci a Najeriya.
Gwamnatin Buhari ta na daf da rabawa ‘Yan Najeriya motoci 2, 000 - Minista
George Akume. Ministan harkokin musamman ya ce za a ceto mutum miliyan 100 daga talauci. An fara shirin yadda za a ceto mutanen kasar daga talauci a yanzu.
Tsohon Shugaba Jonathan ya sake ganawa da Buhari, sun yi kus-kus a fadar Aso Villa (Hotuna)
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya da Goodluck Jonathan su na kokarin ganin an samu zaman lafiya a Mali. A jiya ne Tsohon Shugaba Jonathan ya sake zuwa Villa.
APC ta tafka babbar asara: Kotu ta soke nasarar dan majalisar Kwara, ta ba PDP
Kotun zabe ta tsige dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Kwara, Adam Rufai, ta bai wa dan PDP.
Gwamnoni 36 sun shigar da karar Shugaban kasa Buhari a gaban babban kotun Najeriya
Gwamnoni sun kai karar gwamnatin tarayya a babban kotun koli na kasa. Sun ce dokar 0010 ta ci karo da tsarin mulkin kasar nan, don haka sai ayi fatali da ita.
Zaben 2023: Wasu manyan PDP su na shirin farfado da tsohon Shugaban kasa Jonathan
‘Yan Arewa za su yi Goodluck Jonathan idan shugaba Muhammadu Buhari ya gama mulki 2023. An fara sabon lissafin Jonathan ya sake dawowa kan mulki a Najeriya.
Yarima ya fito ya yi magana game da rade-radin nada shi sabon Sarkin Zazzau
A jiya da yamma Maniru Jafaru ya yi magana a kan nada shi Sarkin Zariya. San Turakin Zazzau ya ce bBabu gaskiya a jita-jitar an nada Yariman Sarkin Zazzau.
Magu: Ina da na-sanin karbar aikin binciken tsohon Shugaban hukumar EFCC - Alkali
Ayo Salami ya yi da-na-sanin shugabantar kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa don bincikar tsohon shugaban hukumar EFCC watau Mista Ibrahim Magu.
Shugaban kasa Buhari ya na yunkurin kashe kamfanin NNPC da Hukumar PPPRA
Mun ji kishin-kishin, shugaban kasa ya kai kudirin PIB gaban Majalisar. Idan kudirin ya zama doka, gwamnati za ta yi watsi da kamfanin man NNPC da irinsu PPPRA.