Yan ta'addan ISWAP sun kai mumunan hari barikin Sojoji a Yobe

Yan ta'addan ISWAP sun kai mumunan hari barikin Sojoji a Yobe

- Bayan harin Damasak, yan Boko Haram sun sake kai hari barikin Sojoji

- Wannan karon yan ta'addan sun kai harin lokacin da sojoji suka fita sinitir

- Sun kona motocin yakin Soji tare da tarwatsa kayayyakin aiki

Yan ta'addan ISWAP sun kai hari barikin Sojin Kumuya dake jihar Yobe ranar Asabar, 17 ga Afrilu, 2021 inda suka lalata manyan makaman hukumar Soji.

Yan ta'addan sun kai harin kwantan baunan ne lokacin jami'an 27 Task Force Brigade da aka tura Buni Gari sun fita sintiri.

PRNigeria ta tattaro cewa yan ta'addan sun dira Kumuya ne tare da taimakon yan gari da masu leken asiri.

Hakazalika an tattaro cewa Sojojin da ake wajen sun yi musayar wuta da yan ta'addan suka suka samu galaba kansu.

DUBA NAN: Garkuwa da dalibai: Gwamnatin Katsina ta tura Karnuka gadin makarantun jihar

Da duminsa: Yan ta'addan ISWAP sun kai mumunan hari barikin Sojoji a Yobe
Da duminsa: Yan ta'addan ISWAP sun kai mumunan hari barikin Sojoji a Yobe @prnigeria
Asali: Twitter

DUBA NAN: Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo

"Yan ta'addan sun kawo mana hari da safiyar Juma'a. Sun far ma barikin yan sanda kuma sun banka mata wuta. An kashe Sojoji 3, a jikkata 1, yayinda aka nemi 171 aka rasa," wata majiya ta bayyanawa Sahara Reporters.

"An kona motar MRAP, an kona bindigar 105MMPH Artillery, Igwa T72 daya," wata majiyar ta bayyana.

Kawo yanzu ba'a san gaba adadin mutanen da harin ya shafa da.

Asali: Legit.ng

Online view pixel