Fitaccen sanatan PDP ya bayyana dalilin da ya sa ba lallai ne a gudanar da babban zaben 2023 ba

Fitaccen sanatan PDP ya bayyana dalilin da ya sa ba lallai ne a gudanar da babban zaben 2023 ba

- Sanata Abaribe ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta gyara matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu

- Dan majalisar na PDP ya ce idan matsalar tsaro ta ci gaba, ba lallai ne a gudanar da babban zaben da ke tafe a 2023 ba

- Abaribe ya caccaki gwamnatin APC da Buhari ke jagoranta, yana mai cewa ta kasa magance matsalar tsaron kasar

Sanata Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya ce ba za a iya gudanar da babban zaben 2023 ba idan har ba a magance matsalar tsaro a kasar nan yadda ya kamata ba.

Ababribe wanda ke wakiltar Abia ta Kudu a majalisar dokoki tarayyar ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Daily Sun ta wallafa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Na sauya masu tsattsauran ra'ayi sama da 1000 tare da koyarwar addinin Islama, Pantami ya fadawa 'yan Najeriya

Fitaccen sanatan PDP ya bayyana dalilin da ya sa ba lallai ne a gudanar da babban zaben 2023 ba
Fitaccen sanatan PDP ya bayyana dalilin da ya sa ba lallai ne a gudanar da babban zaben 2023 ba Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya ce kusan dukkan sassan kasar ba su da kwanciyar hankali, a yankin kudu wanda a baya ya kasance mai kwanciyar hankali.

Sanatan ya ce:

"Abu mafi mahimmanci a yau shi ne, ba mu san ko babban zaɓen na 2023 zai yiwu ba. Mutane suna ta magana.

"Akwai tsoron ta’addanci. Babbar matsalar yanzu ita ce rashin tsaro. Ba ma so mu yi watsi da abin da zai iya karya kasar kuma mu mai da hankali kan batutuwa na lokaci-lokaci kamar zabukan da watakila ba za a yi ba."

Ababribe ya koka kan yadda kudu maso gabashin kasar da ke da tsaro a baya yake fuskantar karuwar ta’addanci a yanzu.

KU KARANTA KUMA: A karshe Isa Pantami ya magantu, ya bayyana dalilin da yasa yake alakanta shi da ‘yan ta’adda

Sanatan na PDP ya zargi Gwamnatin da Buhari ke jagoranta da rashin cika alkawarinta na magance rashin tsaro.

Ya ce:

"Shekaru shida a jere, ya tabarbare. Akwai bukatar mu fada musu cewa su yi kokari su gyara matsalar."

A wani labarin, gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya yi fashin baki kan musayar kalaman dake faruwa tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da Ministar Kudi, Zainab Ahmed.

A makon jiya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Amma a ranar Laraba Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya maras tushe da asali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel