Yanzu-Yanzu: Gwamna Makinde ya sauke shugaban jami'ar LAUTECH

Yanzu-Yanzu: Gwamna Makinde ya sauke shugaban jami'ar LAUTECH

- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sauke shugaban jami'ar LAUTECH, Farfesa Micheal Ologunde

- Olasunkanmi, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a

- Gwamnan ya umurnin Farfesa Ologunde ya mika mulki ga jami'in da ke biye da shi a mukami domin cigaba da gudanar da harkokin jami'ar

Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya sauke shugaban Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Farfesa Micheal Ologunde kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Olasunkanmi ya fitar a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Matawalle ya ɗauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta

Yanzu-Yanzu: Gwamna Makinde ya sauke shugaban jami'ar LAUTECH
Yanzu-Yanzu: Gwamna Makinde ya sauke shugaban jami'ar LAUTECH. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Wasikar ta ce, "Mai girma Injiniya Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo kuma mai ziyara a jami'ar Ladoke Akintola, ya umurci shugaban jami'ar Farfesa M.O. Ologunde ya sauka daga mukaminsa.

"Kazalika, an umurci shugaban jami'ar ya mika mulki ga jami'in da ke biye da shi a muƙami domin cigaba da gudanar da harkokin jami'ar."

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Ƴan Sakai sun bindige ƴan bindiga da dama a tsakiyar kasuwa a Zamfara

A baya, Makinde ya zargi shugaban jami'ar da ingiza ma'aikata su nemi a biya su albashin da suke bi bashi.

Makinde ya ce ya yi mamakin yadda ma'aikatan jami'ar suka fara magana kan albashin bayan an warware matsalolin da suka taso a jami'ar.

Gwamnatin na jihar Osun ta karɓe ragamar gudanarwa na jami'ar da a baya mallakar gwamnatocin Oyo da Osun ne.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel