Da duminsa: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m

Da duminsa: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m

- Iyayen daliban kwalejin aikin noma dake Kaduna, sun ce masu garkuwa da 'ya'yansu suna neman N500m

- Kamar yadda mai magana da yawun iyayen ya sanar, tuni 'yan bindigan suka fara tuntubar iyayen daliban

- Ya ce suna cikin wani hali hadi da yadda gwamnatin jihar Kaduna ta nuna ba zata ceto musu 'ya'yansu ba

Iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar 'ya'yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su.

An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan 'ya'yansu, Vanguard ta wallafa.

Duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021.

A yayin tattaunawa da manema labari a Kaduna a ranar Juma'a, mai magana da yawun iyayen daliban, Friday Sani, ya ce 'yan bindigan sun fara kiran iyayen domin karbar kudin fansa.

KU KARANTA: 2023: Nan babu dadewa wasu gwamnonin PDP zasu dawo APC, Yahaya Bello

Da duminsa: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m
Da duminsa: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m
Asali: Original

KU KARANTA: Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP

Kamar yadda yace, "Halin da muke ciki a yau na tashin hankali ne kuma muna kira ga duniya da su taimaka mana. Mun yi zanga-zanga kuma gwamnatin jihar Kaduna ta kira mu. Mun yi tunanin zamu ji labari mai dadi amma sai aka sanar damu cewa za a hukunta duk wanda yayi sasanci da 'yan bindiga."

"Wannan ne yasa muka sake fitowa a karo na biyu domin sanar da duniya halin da muke ciki duk da an kama mana tunani tare da mallakemu ta yadda aka sace 'ya'yanmu.

"Tuni dama gwamnati ta kama mu, wasu daga cikinmu basu iya bacci ko cin abinci yayin da wasu suka samu ciwuka, don haka babu kamen da yafi haka," Yace.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta damke wani likita tare da wasu mutum 7 a kan zarginsu da ake yi da taimakawa 'yan bindiga a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya bayyana wannan a jawabin da yayi wa manema labarai a Gusau a ranar Alhamis inda yace an kama likitan a kauyen Kamarawa dake karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Kwamishinan yace jami'an rundunar Operation Puff Adder ne suka kama likitan a zarginsa da suke masa na samar da kayan sojoji ga 'yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel