Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa

Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa

- Ma'aikata a karamar hukumar Doma sun yi zanga-zanga saboda rashin biyansu albashi na watanni biyu

- Fusatattun ma'aikatan sun tare titi sun hana mataimakin gwamnan jihar da ayarinsa wucewa

- Mr Rabo Sani, shugaban karamar hukumar Doma ya bawa ma'aikatan hakuri inda ya ce karancin kudi ne yasa ba a biya su ba

Ma'aikatan karamar hukumar Doma na jihar Nasarawa a ranar Juma'a sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu albashi na watanni biyu da kuma zargin cire musu N20m daga albashinsu da Hukumar Samar da Gidaje na Gwamnatin Tarayya ta yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa fusatattun ma'aikatan sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan jihar Dr Emmanuel Akabe wanda dan asalin garin Doma ne.

Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa
Fusatattun ma'aikata sun tare ayarin motoccin mataimakin gwamnan Nasarawa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Akabe tare da shugaban karamar hukumar, Mr Rabo Sani sun gana da ma'aikatan inda suka roke su da su kwantar da hankulansu su kara hakuri.

Sun shaidawa ma'aikatan cewa gwamnatin jihar tana duk mai yiwuwa domin ganin an magance kokensu amma ma'aikatan sun ki kula su a lokacin da suka tare hanyar.

Majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa ma'aikatan sun fara tare hanyar ne daga ranar Litinin na wannan makon inda suke yin 'addu'o'i' na musamman a tsakiyar titi.

Shugaban karamar hukumar ya ce laifin magabatansa ne yasa ba a iya biyansu albashin ba inda ya kara da cewa daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba yana kara lalata lamarin.

A cewarsa, "Ban dauki ma'aikaci ko daya ba, amma magabata na sun yi kuskure, sun dauki ma'aikata fiye da 500."

KU KARANTA: Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina

Ya ce karancin kudi ne yasa ba a biya ma'aikatan ba kuma matsala ce da ta shafi jihar baki daya.

A kan maganar kudin tsarin siyan gidajen na gwamnatin tarayya, ya ce kudaden ba su bace ba, inda ya ce karamar hukuma ta karbi aron kudin ne domin biyan albashi.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel