Khadimul Islam: Gwamna Ganduje ya yi sulhu tsakanin Dangote da AbdulSamad Isyaka Rabiu

Khadimul Islam: Gwamna Ganduje ya yi sulhu tsakanin Dangote da AbdulSamad Isyaka Rabiu

- Kasancewarsu yan asalin Kano, gwamnan Kano ya daidaita tsakanin manyan yan kasuwa biyu

- Dangote da Isyaka Rabiu na kasuwanci iri daya na Siminti, kayan abinci, sukari, dss

Bayan musayar kalamai kan matatar sukari na kamfanin BUA tsakanin manyan attajiran Najeriya biyu, da alamun za'a samu sulhu mai dorewa.

Wannan ya biyo Bayan zaman fahimtar juna da Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, yayi tsakanin shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u bisa kuskuren fahimta da suka samu akan harkokin kasuwancin su.

Wannan ya bayyana ne a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki a shafinsa gwamnan na Facebook ranar Alhamis, 15 ga Afrilu, 2021.

Ya ce: "Hakan ce tasa Gwamnan ya gayyaci yan kasuwar biyu kasancewar su yan asalin jihar Kano da kuma irin gudunmawar da suke baiwa jihar Kano da kasa baki daya."

A cewarsa, manyan attajiran biyu sun karyata rahoton cewa Dangote ya bukaci Isyaka Rabiu su tada farashin sukari.

KU DUBA: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi

Khadimul Islam: Gwamna Ganduje ya yi sulhu tsakanin Dangote da AdulSamad Isyaka Rabiu
Khadimul Islam: Gwamna Ganduje ya yi sulhu tsakanin Dangote da AdulSamad Isyaka Rabiu Credit: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Wadanda suka hallarci zaman sun hada da Hamshakin Dan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ministan ciniki da masana'antu Hon. Niyi Adebayo, wakilin Kano, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, shugaban hukumar NEPZA Hon. Adamu Fanda da shugaban majalisar limaman Juma'a Sheikh Nasiru Adam limamin masallacin Ahmadu Tijjani dake kofar Mata.

Anwar ya ce bayan tattauna muhimman batutuwa da Jan hankali da Gwamna da kuma dattijo Aminu Dantata sukayi an Sami daidaito da fahimtar juna tsakanin manyan yan kasuwar biyu inda sukayi Alkawarin dinke dukkanin rashin fahimtar dake tsakanin su.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

Mun kawo muku labarin cewa kamfanin BUA ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya, rahoton TheCable.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana'antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saba tsarin sukari na Najeriya (NSMP).

Isyaka Rabiu ya ce Dangote da Coumantaros na kokarin "fito-na-fito da umurnin shugaban kasa da kuma mutuncin ma'aikatar kasuwanci da masana'antu."

Kowa ya san cewa "a Najeriya da duniya, duk inda Dangote dake harka ko kasuwanci bai san ganin kowa a wajen kuma ya kan yi iyakan kokarinsa wajen dakile mutum" kuma "hakan yake sake yi yanzu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel