Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa

Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa

- Wani Bishop a Cocin Katolika na Yola, ya jaddada dalilin da ya sa ya kamata a samu hadin kai tsakanin Kirista da Musulmai

- Bishop din ya bayyana cewa ya gina masallaci ga musulmai 'yan gudun hijira a Yola bisa hadin kai

- A cewarsa, kiristoci da yawa suna adawa da shawarar da ya yanke game da aikin masallacin amma bai saurara ba

Bishop na cocin Katolika na Yola, Revd. Fr. Stephen Mamza, ya bayyana cewa ya gamu da adawa lokacin da ya bayyana aniyarsa ta gina masallaci ga Musulmai 'Yan Gudun Hijira a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Mamza, wanda ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Punch, ya ce da farko, ba su nuna wariya ga kowa ba lokacin da shi da sauran mambobin cocin suka dauki bakuncin 'yan gudun hijira.

KU KARANTA: Ba kungiyar IPOB bane ta kashe Hausawa 7 mahauta a Imo, in ji shugaban Hausawa a Imo

Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa
Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa malamin ya ce ba su tambayi addinin da ‘yan gudun hijirar ke bi ba ko kuma su nemi cocinsu da suke bauta, ya kara da cewa an dauki 'yan gudun hijirar a matsayin ’yan Adam da ke bukatar taimako.

Ya ce yawancin 'yan gudun hijirar da suka yi tururuwa zuwa sansaninsu Kiristoci ne amma ya lura cewa akwai kuma adadi mai yawa na Musulmai a cikinsu.

Manza ya jaddada cewa idan har za su iya gina gidaje ga dukkansu, sannan kuma sun gina coci ga Kiristocin da ke cikinsu, yana mai cewa kawai magana ce ta adalci da gaskiya su ma su samar da sararin yin ibada ga Musulmin da ke cikinsu su.

Malamin ya ce:

"Akwai kimanin iyalai 10 zuwa 12 na musulmin a sansanin. Na dai ji kawai tunda ba mu bar musulmai ba yayin samar da abinci ga kiristoci ko barin musulmai yayin da muke gina gidaje ga kiristoci, adalci ne mu gina masallaci ga Musulmai kamar yadda muka gina coci ga Kiristoci.
"Ba wani abu ba ne wanda aka saba yi ba; ba wani abu ne da muka ji ana yi ba, musamman a kasarmu Najeriya, inda kowa yake mai da hankali game da nasu addini."

Ya ce mutane ba su ga hakan a matsayin kyakkyawar niyya ba, yana mai jaddada cewa wasunsu ma sun nuna cewa maharan Boko Haram Musulmai ne kuma sun yi musu barna mai yawa.

"Amma na ce, Da kyau, ba duk musulmai bane Boko Haram (membobi) ba, ba dukkansu banr (musulmai) miyagu.
"Wadanda na sani, wadanda muke tare kuma muke kulawa dasu tsawon shekaru bakwai da suka gabata, na san su na kwarai. Don haka, babu wani dalili da zai sa na nuna musu wariya.
"Ina ganin wannan shi ne dalilin da ya sa muka gina masallacin. Har ma mutane na tambaya, Me ya sa kai Kirista, za ka gina masallaci? Amsar da zan ba su ita ce, Ni Kirista ne, fasto, bishop ne kuma malami, bai kamata in hana kowa hakkinsa na yin ibada ba."

KU KARANTA: Kuskurenku shine zaben Buhari, nasan ba zai iya yin komai ba, Yakasai ga 'yan Najeriya

A wani labarin, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana kaunar mutanen Ogbia, wata karamar kabilar Ijaw a cikin jihar Bayelsa.

Ministan ya ce dalili kuwa daya ne, saboda dansu, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya bar masa mulki cikin lumana a 2015, The Nation ta ruwaito.

Sylva ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya ke duba aikin da ake yi na samar da Man Fetur da Gas na Kasa (NOGaPS) wanda Hukumar NCDMB ke ginawa a Emeyal 1, karamar hukumar Ogbia ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel