Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

- Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dr. Godwin Emefiele ya bayyana babban dalilin da yake tilasta gwamnati ta ciyo bashi

- Gwamnan ya ce ciwo bashi ba laifi bane kuma ba zunubi bane, amma akwai wajabcin sanya ido a kan ƙuɗin da aka amso da kuma hanyar da aka yi amfani da su

- Ya ce mafi yawan lokuta idan ka duba kuɗin da gwamnati ke samu da kuma kuɗin da take kashewa zakaga cewa ciyo bashi ba laifi bane

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce Najeriya ba zata taɓa daina ciwo bashi daga waje ba musamman idan ya zama dole ba yadda zata iya saboda tana son cika kasafin kuɗi.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa kan batun bashin da ake bin Najeriya wanda aka yi wa take da 'Hauhawar asusun bashin Najeriya da ƙalubalen da yake dashi ga cigaban ƙasa' wanda ƙungiyar bada taimakon farko (AAN) ta shirya.

Taron ya ƙunshi ƙungiyar ta AAN da kuma masu ruwa da tsaki a al'amuran rancen kuɗi a Najeriya.

Kuma an shirya taron ne don nuna damuwa kan rashin tabbas ɗin ciwo bashi da kuma hauhawar asusun bashin Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Buhari.

A jawabin gwamnan, wanda mataimakin Daraktan sashin kula da tsare-tsaren kuɗi na bankin, Dr. Tawose Joseph, ya wakilta, ya ce ciyo bashi ba laifi bane amma akwai buƙatar san ya ido akan ƙuɗin da aka ciyo bashin da kuma dalilin hakan.

Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi
Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi Hoto: @NNPCgroup
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa, rancen kuɗi a gwamnatance yana daga cikin ginshiƙin gudanar d kasafin ƙasa, kuma ciyo bashi b laifi bane kuma ba zunubi bane.

KARANTA ANAN: Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa

Gwamnan ya ce ko ma'aikatu masu zaman kansu suna ciyo bashi doɓ sun cigab da gudanar da ayyukan su, sai dai babban abun damuwar shine dalilin ciyo bashin d kuma abinda aka yi da kuɗin ciyo bashin.

Gwamnan CBN ɗin ya ce idan ka duba nawa gwamnati ke samu kuma nawa take kashewa zaka fahinci cewa ciyo bashi na daga cikin aikin gwamnati.

Ya kuma ƙara da cewa, CBN ya fahinci matsalolin dake tattare da ciyo bashi, kuma hakan babban ƙalubale ne ga ƙasa.

Wannan ne ma yasa babban bankin ya ƙirƙiro da sabbin dabaru da tsare-tsare don fahimtar da talakawan Najeriya.

Ya ce CBN ya ƙaddamar da tsare-tsare 37 waɗanda zasu taimaka matuƙa wajen farfaɗo d tattalin arziƙi, amma ya bayyana cewa akwai babban ƙalubale kan shirin CBN ɗin.

A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa sun bukaci IGP mai rikon kwarya da ya gaggauta kawo karshen ta’addanci

Gwamnonin Arewa sun nemi mukaddashin sufeto janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali, da ya zaunar da kasar nan lafiya.

Shugaban kungiyar, Simon Lalong, ya yi kiran ne a ranar Asabar, 10 ga Afrilu, a cikin sakon taya murna ga sabon shugaban ‘yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel