Fashola: Za a Kammala babban titin Lagos zuwa Ibadan a 2022

Fashola: Za a Kammala babban titin Lagos zuwa Ibadan a 2022

-A cigaba da ayyukan titinun ƙasar nan da gwamnatin tarayya ke yi.

-Fashola ya tabbatar da cewa za a kammala titin Ikko-Ibandan a shekarar 2022.

-Ya bayyana hakan ne dai a wata zantawa da yi da manema labarai.

A ruwayar The Punch, ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya tabbatar da cewa za a kammala babban titin Ikko zuwa Ibadan a farkon shekarar shekarar 2022.

Ya faɗi hakan ne a wata zantawa da ya yi a ranar lahadi da gidan radiyon Bond FM.

a cewarsa, rashin saurin aiki ya faru sakamakon rashin damar rufe titin gaba ɗaya da gwamnati ta yi.

Karanta wannan: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

Fashola: Za a Kammala babban titin Lagos zuwa Ibadan a 2022
Fashola: Za a Kammala babban titin Lagos zuwa Ibadan a 2022. Tushe: Businessday.ng
Asali: Twitter

Ya tabbatar da cewa kilomita 80 cikin 127 ya kammalu gaba ɗaya, inda yai kira ga masu amfani da hanyar su ƙara yi wa gwamnati haƙuri.

Ministan ya ce. "A yanzu da muke magana da ku, an kammala kilomita 80 kuma mafi yawan na ɓangaren titin da ake amfani da yau an kammala shi."

"Sai dai ba za mu iya rufe hanyar ba gaba ɗaya. Adadin ababen hawa da ake amfani da su sun kusa dubu huɗu. Wanna ta sa ba za mu iya rufe hanyar Ikko zuwa Ibadan ba kacokan. Ya kamata a kammala aikin titin a shekarar 2022.''

"Da yake mun iya rufe hanyar 'Third Mainland Bridge,' shi ya sa nan da nan muka kammala aikinsa."

Karanta wannan: Burutai: ƴan Najeriya sam ba sa yaba wa ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance matsalar tsaro

An ba da aikin kwangilar hanyar ta Ikko zuwa Ibadan a shekarar 2013 ga kanfanoni biyu.

Julius Berger ne ke aikin ɓangare guda wacce ta miƙa daga Ojota na Ikko zuwa Sagamu, inda kuma RCC ke aikin daga Sagamu zuwa Ibadan.

A wani labarin kuma, Abubakar Bello, gwamnan Neja, ya ce jiharsa ba ta biya fansa ba don sakin dalibai da malamansu da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, TheCable ta ruwaito.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, ‘yan bindiga sun far wa makarantar GSC Kagara kuma suka yi awon gaba da dalibai, ma’aikata, da danginsu.

Wadanda aka sacen da aka saka a ranar Asabar, an tarbe su ne a gidan gwamnatin jihar dake Minna, babban birnin jihar Neja.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel