Kotu ta bada umarnin kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan Zamfara

Kotu ta bada umarnin kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan Zamfara

- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden bankunan Abdulaziz Yari

- Kotun ta bada wannan umarnin ne sakamakon maka tsohon gwamnan kotu da hukumar ICPC tayi

- Alkalin kotun ya ce bai ga dalilin da zai hana hukumar ICPC kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan ba

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar da yadda wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden da ke bankuna na tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

Kudaden sun hada da wadanda ke bankunan Zenith da Polaris na kasar Najeriya, BBC Hausa ta wallafa.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran ya ruwaito, kudaden da ke bankin Polaris sun kai dala hamsin da shida.

Akwai Naira miliyan 12.9, Naira miliyan 11.2, dala 30,309.99, Naira 217,388.04, dala 311,872.5 wadanda aka adana a bankin Zenith duk da sunan tsohon gwamnan da kamfanoninsa.

Kotu ta bada umarnin kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan Zamfara
Kotu ta bada umarnin kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan Zamfara. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon saurayi da abokansa suna jibgar budurwarsa bayan sun kama ta da kato

Kamar yadda alkalin kotun ya yanke, ya ce babu dalilin da zai sa hukumar ICPC wacce ta shigar da karar ta kasa kwace kudaden.

Idan za mu tuna, hukumar ICPC tana zargin tsohon gwamna Abdulaziz yari da samun makuden kudaden ta haramtacciyar hanya.

KU KARANTA: Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bude makarantun gaba da sakandare na jihar a ranar Litinin, 25 ga watan Janairun 2021 a fadin jihar baki daya.

Amma kuma ta ja kunnen dukkan hukumomin makarantun da su kasance masu kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona da jihar ta Gindaya, Daily Trust ta tabbatar da hakan.

A wata takardar da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar kuma ta samu sa hannun babbar sakatariyar ma'aikatar, Phoebi Sukai Yayi, an bayyana cewa wannan amincewar ta biyo bayan tura kungiyar dubawa tare da tantancewa dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar, wadanda suka tabbatar da cewa makarantun sun shirya kuma sun kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel