Yan bindiga sun kashe mace mai juna biyu na watanni 8 a Kaduna

Yan bindiga sun kashe mace mai juna biyu na watanni 8 a Kaduna

- 'Yan bindiga sun yi ajalin wata mata ma'aikaciyar lafiya mai juna biyu na watanni 8 a Kaduna

- Matar, Aisha Yusuf tana cikin motar haya ne tare da fasinjoji a hanyar Birnin Gwari a lokacin da yan bindigan suka bude wa motar wuta

- Dan uwan marigayiyar ya tabbatar da rasuwarta inda ya ce mutuminyar kirki ne wadda mutane ke kaunarta saboda jajircewarta wurin aiki

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe wata mata mai cikin watanni 8 kuma ma'aikaciyar lafina a titin Kaduna zuwa Birnin Gwari bayan bude wuta a motar hayar da ta ke ciki da ke hanyar zuwa Kaduna.

An kashe ta ne a hanyarta na zuwa Kaduna a wani wuri da ake kira Zankoro kafin a karasa Unguwan Yako a ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Yan bindiga sun kashe mace mai juna biyu na watanni 8 a Kaduna
Yan bindiga sun kashe mace mai juna biyu na watanni 8 a Kaduna. Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden

An gano cewa 'yan bindigan sun bude wa motar hayar wuta ne da rana a kokarinsu na tsayar da motar.

Dan uwan marigayiyar, Aliyu Mahmud ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin ta wayar tarho inda ya ce sunanta Aisha Yusuf.

Ya bayyana ta a matsayin ma'aikaciyar lafiya mai bada gudun mawa a garin Birnin Gwari.

"Tana da ciki na wata takwas amma ta kasance mai jajircewa wurin aiki a cibiyar lafiya bai daya inda ta ke aiki a Birnin Gwari. Mafi yawancin mutanen garin na kaunar ta sosai saboda jajircewarta duk da cewa ita ma'aikaciya ce mai bada gudunmawa," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa

Ya ce yan bindigan sun bude wa motar da ke dauke da ita da sauran fasinjoji wuta a hanyarsu ta komawa Kaduna.

Da aka tuntube shi, kakakin 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin kiran DPO na yankin domin samun karin bayani kafin ya yi tsokaci a kan lamarin.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel