Masu garkuwa da mutane sun kame wanda ya kawo kudin fansar 'yan uwansa

Masu garkuwa da mutane sun kame wanda ya kawo kudin fansar 'yan uwansa

- 'Yan bindiga sun kame wani wanda ya kai kudin fansar 'yan uwansa da a ka sace

- 'Yan bindigan sun bukaci sai an sake tura musu Naira miliyan daya kafin su sake mutumin

- A halin yanzu mutanen yankin wadanda a ka sacen suna zaman dardar din zuwa gonakansu

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wani mutum, Solomon Isaac, bayan sun amshi N600,000 daga gare shi domin sakin wasu mutane biyu da aka sace a hannunsu a yankin Rubochi Sabo da ke Gadabuke, karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

Wani dangin wanda abin ya shafa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata, bayan da Isaac ya je ya ba da kudin fansa ga masu satar ‘yan uwansa maza biyu, Usman Emmanuel da Thanksgod Emmanuel.

An sace mutanen biyu a ranar 4 ga watan Janairu, 2021 a wata gona a cikin yankin, Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA: Wasu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum

Masu garkuwa da mutane sun kame wanda ya kawo kudin fansar 'yan uwansa
Masu garkuwa da mutane sun kame wanda ya kawo kudin fansar 'yan uwansa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa 'yan uwan ​​biyu suna girbin doya ne a lokacin da 'yan bindigar suka mamaye gonarsu suka tafi da su.

Ya ce dangin sun yi kokarin tara N600,000 bayan tattaunawa mai karfi da masu satar wadanda suka dage kan karbar Naira miliyan biyu a baya.

"Don haka ne bayan da iyalen suka sami damar tattaunawa da su har tsawon mako guda, kafin yanzu suka amince su karbi N600,000, amma lokacin da Isaac ya je kai kudin fansa sai suka yi garkuwa da shi," in ji shi.

A cewarsa, masu garkuwan sun saki daya daga cikin wadanda aka sacen da farko daga bisani suka yi garkuwa da Isaac bayan sun karbi N600,000.

Ya ce masu garkuwan suna neman kudin fansa miliyan N1 kafin a saki Isaac da wani mutum daya da aka sace.

“A gaskiya, a yanzu da nake magana da ku, dangin sun rikice game da inda za su samo wata Naira miliyan daya don ganin an sako mutanen biyu da aka yi garkuwar da su, bayan da su (masu garkuwar) suka amshi N600,000,” in ji shi.

Wani mazaunin kauyen Kande da ke makwabtaka da yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce wadanda ake zargin masu satar mutane suna da filin kwana a kusa da yankin.

Ya kara da cewa manoma a yanzu suna fargabar zuwa gonakinsu don girbar amfanin gonarsu saboda tsoro.

KU KARANTA: 2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna

"Kuma ina so in fada muku cewa wadannan masu satar mutane galibinsu sun fito ne daga kauyukan da ke makwabtaka da yankin Kuje a cikin FCT saboda a can ne akwai manyan dazuka da za su yi hari a nan su koma maboyarsu," in ji shi.

Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Nasarawa ASP Ramhan Nansel, bai amsa kiran waya ba ko amsa sakon tes da aka tura zuwa wayar sa don tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin daban, 'Yan kasuwar Kantim Kwari goma sha takwas da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Aba a jihar Abia sun an sake su dakyar.

Ku tuna cewa an sace yan kasuwar ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Janairu, a Okene, jihar Kogi, akan hanyarsu ta zuwa Aba don siyan kayan masaku.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Arewa na Najeriya, Alhaji Abubakar Babawo ya tabbatar da sakin 'yan kasuwar a wata hira ta wayar tarho da jaridar The PUNCH a Kano ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel