Oyedepo: Lai da Gbemi Saraki, ba su goyon bayan tsige Bolarinwa da aka yi

Oyedepo: Lai da Gbemi Saraki, ba su goyon bayan tsige Bolarinwa da aka yi

- Uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta sauke Majalisar Bashir Bolarinwa a jihar Kwara

- Wadanda basu tare da Gwamnan Kwara sam ba su goyon bayan wannan mataki

- Masu yi wa Gwamnan hamayya su na barazanar maimata abin da ya faru a 2019

Rigimar cikin gidan da APC ta ke fama da ita a jihar Kwara ta rikide, bayan an sauke Bashir Bolarinwa daga kan kujerar shugaban jam’iyya na jiha.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa ministocin yada labarai da na sufuri, Lai Mohammed da Gbemisola Saraki ba su goyon bayan wannan mataki.

Alhaji Lai Mohammed da Gbemisola Saraki da yaransu sun bayyana wannan matsaya ne ta bakin Akogun Iyiola Oyedepo wanda ya yi jawabi a makon nan.

A jawabin da Akogun Iyiola Oyedepo da wasu mutane 19 suka sa wa hannu, sun ja kunnen mai girma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak.

KU KARANTA: Lai Mohammed da Saraki sun huro wa Gwamnan Kwara wuta

Oyedepo: Lai da Gbemi Saraki, ba su goyon bayan tsige Bolarinwa da aka yi
Ana zargin AbdulRahman AbdulRazaq da hannu a tsige Bolarinwa Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

“Gbemi Saraki da Lai Mohammed suna tare da mu gam. Ba su tare da gwamnan, kuma mu na fadawa Duniya wannan a fili.” Inji Akogun Oyedepo.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun yi ikirarin tun da har su ka fatattaki Bukola Saraki a 2019, sauke Abdulrazak daga kan mulki ba zai yi masu wahala ba.

Wadanda suka sa hannu a wannan jawabi sun hada da T. A Sunday Oyebiyi, Umaru Sha’aba, Isa Bio lbrahim, Ladi Mustapha, M. T. Mamman da Akande Adefila.

Ragowar sune: Saheed Popoola, Shuaib Abdulraheem, Ahmed Zuru, Lukman Mustapha, Waziri Olayiwola Gobir, Saliu Mustapha, SY Abdullahi, da Tajudeen Audu.

KU KARANTA: Rigimar siyasar Gwamna Makinde da Mataimakinsa ta kara kamari

Sai kuma Akeem Lawal, Alhaji Bolaji Jimoh, Nasiru Mohammed Efuman da H. B. Oyedepo.

Daga baya bangaren gwamna ta bakin Kunle Suleiman, sun yi raddi, su na nuna goyon bayan matakin da uwar jam’iyya ta dauka na ruguza majalisar Bolarinwa.

A yau ne mu ka ji cewa wata gamayyar kungiya tayi watsi da irinsu Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, ta roki Bala Mohammed ya nemi takarar Shugaban kasa.

Shugaban kungiyar COCSOTRAGG ya yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi ya yi takarar Shugaban kasa.

Kwamred Raphael Terkula, ya ce Najeriya tana bukatar shugaban da zai iya fuskantar matsalolin kasar nan. Kuma Bala Mohammed shi ne ya dace da wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel