COCSOTRAGG ta yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi ya yi takarar Shugaban kasa

COCSOTRAGG ta yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi ya yi takarar Shugaban kasa

-Kungiyar COCSOTRAGG tace Sanata Bala Mohammed ya dace ya rike Najeriya

-Raphael Terkula yace sun samu ‘dan siyasar bai da kabilanci ko nuna son-kai

-Wannan kungiyar tace tsohon Ministan na Abuja ya cancanci yin takara a 2023

A ranar Laraba, 13 ga watan Junairu, 2020, kungiyar COCSOTRAGG ta fito ta na kira ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nemi babbar kujera.

Jaridar Sun News ta rahoto wannan kungiya ta COCSOTRAGG tana cewa akwai bukatar Sanata Bala A. Mohammed ya yi takarar shuagaban kasa a zaben 2023.

Shugaban wannan kungiya na reshen jihar Benuwai, Kwamred Raphael Terkula, ya ce Najeriya tana bukatar shugaban da zai iya fuskantar matsalolin kasar nan.

Da yake magana a garin Benuwai, jihar Benuwai, Raphael Terkula yace ganin yadda Mohammed ya rike Minista na tsawon shekara shida, zai iya rike Najeriya.

KU KARANTA: 2023: Yadda Hukumar INEC za ta sa kafar wando da masu murdiyar zabe

Jagoran wannan kungiya na shiyyar Arewa maso tsakiya, Orokombu Terngu, ya karanta wannan jawabi a madadin Raphael Terkula a gaban manema labaran.

A ra'ayin Coalition of Civil Society Organizations for Transparency and Good Governance, duk cikin masu neman takara, babu wanda ya fi dacewa irin gwamnan.

“Bayan la’akari da duk manyan ‘yan siyasan da ake da su a yau, COCSOTRAGG ta na da ra’ayin cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya na da abin da ake bukata ya jagoranci Najeriya.”

Kungiyar ta ce Sanata Bala Mohammed zai kai kasar ga ci idan ya samu damar mulki a 2023.

KU KARANTA: 2023 ta barka gidan Gwamnatin PDP, Gwamnan Oyo da Mataimakinsa ana fada

COCSOTRAGG ta yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi ya yi takarar Shugaban kasa
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed Hoto: Twitter Daga: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Terngu ya ce: “Mohammed mutum ne maras kabilanci da kokarin fifita na-kusa da shi, kuma ya kulla alaka da jama’a iri-iri. Ya yi aiki da kowa a lokacin da yake kujerar Minista.”

Mun tattaro maku wasu jerin manyan alkawuran da ake jiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika a shekaru kusan biyun da suka rage masa a kan mulki.

Inganta tattalin arziki da bunkasa harkar noma su na cikin abubuwan da ‘Yan Najeriya suke tsammanin gwamnatin shugaba Buhari za ta yi kafin ya bar ofis a 2023.

Ragowar ayyukan da ke gaban Gwamnatin Buhari kafin nan sun hada yaki da cin hanci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel