‘Yan Sanda masu neman ‘na goro’ sun yi wa Direba tunbur, sun bata masa mota a Fatakwal

‘Yan Sanda masu neman ‘na goro’ sun yi wa Direba tunbur, sun bata masa mota a Fatakwal

- An samu hayaniya tsakanin Direbobi da ‘Yan Sanda a Garin Fatakwal

- Jami’an tsaron sun tube wani Direban mota, sun yi masa sintir kan titi

- Ana zargin an wulakanta wannan mutumi ne saboda kin bada rashawa

Jaridar Punch ta rahoto cewa an yi hayaniya a yankin Ada George a garin Fatakwal, jihar Ribas, yayin da ‘yan sanda su ka ci mutuncin wani direba.

A ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020, wasu gungun ‘yan sanda a Fatakwal, jihar Ribas su ka tare wani direba, su ka cire masa kayan jikinsa.

Wannan abin kunya ya wakana ne a lokacin da jami’an tsaron suka bukaci wannan mutumi mai suna Emenike ya basu cin hancin da su ke karba.

Rahoton ya ce wannan mutumi ya yi taurin-kai, ya ki ba ‘yan sandan cuwa-cuwa, sai su ka tsare shi, su ka tube shi da rana-tsaka, ana ji-ana gani.

KU KARANTA: Hisbah sun cafke masu zaman banza da saida kwayoyi da giya

Sauran direbobi da ke aiki a wannan unguwa a Fatakwal da ke Ribas sun yi bore domin nuna ba su ji dadin wannan abu da aka yi wa abokan aikinsu ba.

Wani shugaban kungiyar Direbobi na shiyyar Choba, Bestman Chile yace ‘yan sanda sun nemi cin hanci da rashawa ne inda Emenike ya ki ba su komai.

Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa ya ce: “Ya shiga motar Emenike, ya fada ya tuka zuwa wajen da ‘yan sanda su ke.”

“A hanyarsa, sai ‘dan sandan ya fara dukansa da sanda, shi kuma ya na kici-kici da shi da wannan mutumi da kan mota."

KU KARANTA: ‘Yan kabilar Ibo suna harin kujerar Shugaban kasa a 2023 gadan-gadan

‘Yan Sanda masu neman ‘na goro’ sun yi wa Direba tunbur, sun bata masa mota a F/Kwal
Kwamishinan 'Yan Sanda na Ribas Hoto: www.olisa.tv
Asali: UGC

“Bayan direban ya tsaida motar, wasu ‘yan sanda su ka zo, su ka fara dukan Emenike, su ka tube shi, su ka yi masa tsirara, su ka lalata masa abin hawa.”

Rahoton ya ce daga nan direbobi su ka rika zanga-zanga a titi, wanda hakan ya jawo cincirindo. Jami’in ‘yan sanda, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da wannan.

Mai ba shugaban kasa shawara a harkar Neja-Delta, Sanata Ita Enang, ya fadi gwamnonin da ke da laifi wajen matsalar rashin tsaro a Kudancin Najeriya.

Sanata Ita Enang ya ce Jihohin da ke da arzikin mai sun yi wasa da karin 13% da ake ba su daga kason FAAC, wanda hakan ya jawo rashin zaman lafiya.

Tsohon Sanatan ya zargi Gwamnonin Neja-Delta da barna da damar da suka samu

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel