Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Wakkala, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Wakkala, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Jam'iyyar APC na cigaba da fuskantar matsaloli a jihar Zamfara

- Wannan rikici ya haddasawa jam'iyyar asarar sukkan kujerun da ta samu a zaben 2019

- Yanzu jam'iyyar ta fara rashin 'yayanta yayinda suka fara guduwa APC

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Wakkala ya bayyana hakan ranar Laraba yayin hira da manema labarai a Gusau, birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.

Ya kasance mataimakin gwamnatin jihar lokacin mulkin tsohon gwamna AbdulAziz Yari.

Yayin bayani kan dalilinsa na sauya sheka, Wakkala ya ce tun lokacin da APC ta rasa mulki a 2019, an daina tuntubarsa kan abubuwan dake gudana a jam'iyyar.

Ya ce tun lokacin da gwamna Bello Matawalle ya hau mulki, ya kasance mai bashi shawara, musamman wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Ya kara da cewa ya rubuta wasika na musamman ga tsohon maigidansa, AbdulAziz Yari, kan shawarar da ya yanke na fita daga APC.

KU KARANTA: Masu mota zasu biya N250,000 a mayar da musu da ita mai amfani da iskar Gas maimakon fetur, Gwamnatin tarayya

Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Wakkala, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Wakkala, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP Cresit: Zamfara_state
Asali: Twitter

A wani labarin daban, mata masu gudun hijira daga kauyakun jihar Zamfara sun ce yunwa da sanyi zai iya ajalin su da yaransu, bayan 'yan bindiga sun kone musu gidajensu.

BBC Hausa ta ruwaito yadda fiye da mutane 500 daga kauyukun karamar hukumar Maru suke ta gararamba a tituna da sansanin gudun hijira na garin Mai Rairai, da ke jihar Kebbi.

Matan da suke sansanin 'yan gudun hijira tare da yaransu, sun ce ba su da abinci kuma 'yan bindiga sun kone musu gonakinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel