Najeriya zata fara fitar da kayyakin man fetur kasashen waje, Buhari

Najeriya zata fara fitar da kayyakin man fetur kasashen waje, Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kadamar da karamin matatatan man fetur na Waltersmith da ke jihar Imo

- Shugaban kasar ya ce samar da wannan matatan man fetur din zai bawa Najeriya damar fara fitar daman fetur zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita

- Buhari ya bayyana gamsuwarsa da aikin matatan man fetur din inda ya ce za a cigaba da aikin fadada wasu matatun

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya zata fara fitar da man fetur da sauran ababen da ake samarwa daga danyen man fetur zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita bayan kafa

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da karamin matatar man fetur mai tace gangan 5,000 duk rana na Waltersmith da ke Ibigwe a Jihar Imo kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Najeriya za ta fara fitar da kayyakin danyen mai - Buhari
Najeriya za ta fara fitar da kayyakin danyen mai - Buhari. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

Buhari ya kuma kaddamar da bude fara aikin fadada matatan man da ake sa ran zai rika tace gangan mai 50,000 a duk rana.

A cewarsa, samar da matatun man na daya daga cikin muhimman bangarori hudu da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai karkashin shirin inganta matatun mai tun a shekarar 2018.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara

Shugaban kasar ya ce ya yi farin ciki da matatan mai na Waltersmith da ke karamar hukumar Ohaji na jihar Imo da aka kammala bayan shekaru biyu da kaddamar da shirin duk da cewa an dade da bawa kamfanoni lasisin kafa matattun man.

"Bugu da kari, aiki yana sauri a sauran wurare uku da aikin farfado da tsofaffin matatu, sauran wuraren da za a samar da wasu matatun.

"Farfado da matatun zai bamu damar zama daya daga cikin manyan masu fitar kayyakin man fetur bawai iya makwabtan kasashe har a kasuwannin duniya.

"Irin wannan matatar ita ce irin ta farko mafi girma a fadin kasar.

"Irin rawar da gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar Nigerian Content Development and Monitoring Board (NCDMB) da kuma matatar Waltersmith, sun taka gagarumar gudunmawa wajen saurin aikin a cewar" a cewar sa.

Buhari ya ce aikin fadada matatar zai taimakawa Najeriya wajen farfado da tattalin arziki a kasar.

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel