Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari

Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari

- Kungiyar dattawan arewa ta ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya ji tsoron Allah da kuma rantsuwar kama aiki da ya dauka

- A cewar kungiyar sarai Buhari ya san illar da ke tattare da rantsuwa da Al-Qur'ani ba tare da cikawa ba

- Kungiyar na magana ne a kan matsalar rashin tsaro da ya addabi al'umman arewacin kasar

Kungiyar dattawa Arewa (ACF) ta bayyana cewa rashin tsaro a yankin arewacin kasar ya kara tabarbarewa tun bayan taronta na karshe a watan Oktoba.

ACF ta bayyana cewa a wannan taron ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya mayar da hankali sosai a kan rashin tsaron da ke yankin.

“A ganinmu babu bukatar kira ga Buhari a kan ya cika alkawaran rantswar da yayi na karban aiki. Ya fi kowa sanin illar rantsuwa da Al-Qur’ani da kuma kin cika abunda mutum yayi wa Allah rantsuwa a kai."

Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari
Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kungiyar ta ce ta damu matuka a kan cewa yan bindiga na ta kashe-kashen mutane a arewa wanda ministan yan sanda “ya yi ikirarin karya na cewa an magance lamarin.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji

“Kawai dai muna jadadda masa fushi da damuwar yan arewacin kasar da dama ne domin ya yi abunda ya dace kuma cikin gaggawa. Lokaci na kurewa.”

Wata sanarwa daga sakataren labaran kungiyar ta kasa, Emmanuel Yewe ta bayyana cewa:

“Duk da cewar ministan ya yi ikirarin karya, imma bisa rashin sani ne ko da gan-gan, na nasara a kan yan bindigan, an kai wa jami’an yan sanda 12 a bakin aiki daga Zamfara zuwa Kano a yayinda suke tuki a jerin gwano hari sannan aka nemi iyalan yan sandan su biya kudin fansa.

“Baya ga wannan, yan bindigan sun sanya shinge a kan hanyan Kaduna-Abuja wanda yan sandan suka yi ikirari sau da dama cewa sun yanto daga yan bindiga.”

Yayinda take Allah wadai da hare-haren babban titin Kaduna-Abuja ciki harda na sace daliban ABU tara, kungiyar ta ce rashin tsaro ya zama abun damuwa ga yan arewa.

Ta ce yan arewacin kasar ne suka zabi gwamnati mai mulki bisa zaton za ta karesu da dukiyoyinsu kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar.

KU KARANTA KUMA: Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni

A gefe guda, Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta ce gwamnati Shugaba Muhammad Buhari ta gaza yin kataɓus don kawo ƙarshen matsalar tsaron arewacin Najeriya.

Ƙungiyar a wani jawabi da ta fitar ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, ta zargi gwamnatin Buhari da yin burus tare da nuna halin ko in kula ga al-ummar yankin Arewa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel