Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna)

- An kaddamar da sabon karamar matatar man fetur a kudancin Najeriya

- Hakazalika shugaba Buhari kaddamar da ginin sabon wani matatan duk na kamfani daya

- Har yanzu ana sauraron attajiri Aliko Dangote ya kammala ginin nasa matatar dake Legas

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron kaddamar da sabon matatar man feturin WalterSmith dake Ibigwe Oil Field, jihar Imo a ranar 24 ga Nuwamba, 2020.

Buhari ya jagoranci taron ta yanar gizo.

Shugaban kasan ya ce ginin wannan sabon matatar man zai taimaka wajen samar da isasshen man feturr a kasa tare da dakatad da saya daga waje.

Matatar man a cewar Buhari, za ta rika tace mai ganga 500 yayinda za'a fara ginin sabo wanda zai rika tace mai gana 45,000 kulli yaumin.

"Samar da hanyar gina matatun mai zai taimaka mana wajen zama masu fitar da mai zuwa ga makwabtanmu da kuma duniya gaba daya, " Buhari yace.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sune gwamnan Imo, Hope Uzodinma; ministan mai, Timipre Sylva; shugaban NNPC, Mele Kyari; Sakataren NCDMB, Simbi Wabote; da shugaban kamfanin WalterSmith, Abdulrazaq Isa.

Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna) Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya

Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da sabon matatar mai a jihar Imo (Hotuna) Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Facebook

KU KARANTA: Allah ya yi wa 'yar Pantami rasuwa

Wannan matatar mai ba mallakin gwamnatin Najeriya bane.

Kamfanin WalterSmith Petroman Oil Limited ke da kashi 70% na hannun jari yayinda gwamnatin Najeriya ke da hannun jarin 30%.

A bangare guda, duk da tsadar da mai ke yi, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba'a gama cire tallafi kan kayayyakin man fetur ba a kasar.

Haka Ministan Man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana a hirar da yayi ranar Litinin da Seun Okinbaloye na Channels TV.

A cewar, wannan kawai somin tabi ne, yanzu aka fara cire tallafi kan kayan man fetur.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel