Ogungbeje ya kai Gwamnatocin Legas da Tarayya kara a gaban kotun tarayya

Ogungbeje ya kai Gwamnatocin Legas da Tarayya kara a gaban kotun tarayya

- Lauya ya na karar gwamnatin tarayya da ta jihar Legas a kotu a Legas

- Olukoya Ogungbeje ya na so a biya ‘yan zanga-zanga da aka harba diyya

- Lauyan ya yi karar AGF, IGP, SSS, Gwamnatin Legas da Shugaban kasa

Wani Lauya mai suna Olukoya Ogungbeje, ya gabatar da karar Naira biliyan 10 a kotu, ya na kalubalantar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Olukoya Ogungbeje ya kuma hada shugaban hafsun sojin kasa, Janar Tukur Buratai da wasu mutane a wannan shari’a a kan harbe ‘yan zanga-zanga.

Lautan ya na ikirarin jami’an tsaro sun bude wa Bayin Allah masu zanga-zangar lumanar #EndSARS wuta a Lekki, a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2020.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta na shirin zaftare farashin ‘data’– NCC

A wannan shari’a da za ayi a gaban kotun tarayya na Legas, Ogungbeje ya roki Alkali ya bayyana harbe-harben da aka yi a matsayin abin da ya saba doka.

Ogungbeje ya na ikirarin harbe masu zanga-zanga ya ci karo da dokar kasa, haramun ne, kuma zalunci ne da wuce gona da iri a tsarin mulkin farar hula.

Rokon da wannan Lauyan ya ke yi a gaban kuliya shi ne a biya wadanda aka yi wa harbin gilla na babu gaira babu dalili Naira biliyan 10 domin su rage zafi.

“Amfani da karfi da harbin 'yan zanga-zangar lumuna keta hakinsu ne na rayuwa da bada damar a sauraresu da shirya taro kamar yadda tsarin mulki ya tanada.”

KU KARANTA: Falana ya fallasa wadanda su ka harbi masu zanga-zanga

Ogungbeje ya kai Gwamnatocin Legas da Tarayya kara a gaban kotun tarayya
Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Lauyan ya ce abin da jami’an tsaro su ka yi ya saba wa sassa 33, 36, 38, 39 da 40 na tsarin mulki.

Sauran wadanda ake kara su ne Sufetan ‘yan sanda, hukumar ‘yan sanda, SSS, darektan SSS, gwamnatin Legas da kwamishinan shari’ar ta da kuma AGF.

Dazu kun ji cewa ana neman duk wanda ya saci kayan tallafin COVID-19 a Jihar Kaduna. Jami’an tsaro sun soma bi gida bayan gida domin su kama barayi a jihar.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba zai yarda da sata da sunan #EndSARS ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel