Yan sanda sun kama mutane 55 yayin zanga-zangar EndSARS a Kano

Yan sanda sun kama mutane 55 yayin zanga-zangar EndSARS a Kano

- Jami'an yan sandan Kano sun kama mutane 55 a yayin zanga-zangar EndSARS a jihar

- An kama mutanen kan zarginsu da ake yi da hannu wajen tayar da zaune-tsaye a unguwar Sabon Gari

- Rahoton ya kuma bayyana cewa an same su dauke da muggan makamai tare da fasa shagunan mutane da yi masu sata

Rundunar yan sanda ta jihar Kano, ta tabbatar da kama mutane 55 bisa zarginsu da ake da hannu wajen tayar da kayar baya a unguwar Sabon Gari da ke birnin jihar, a yayin zanga-zangar EndSARS.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema Labarai a yau Lahadi, 25 ga watan Oktoba.

Kiyawa ya bayyana cewa an damke mutanen ne, saboda kama su da aka yi dauke da makamai da suka hada da adduna, wukake, gorori da kuma bindigogi.

Har ila yau an kama su da laifin fasa shagunan mutane tare da debe kayayyakin da ba nasu ba, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu

Yan sanda sun kama mutane 55 yayin zanga-zangar EndSARS a Kano
Yan sanda sun kama mutane 55 yayin zanga-zangar EndSARS a Kano Hoto: 247ureports.com
Asali: UGC

Kakakin yan sandan ya kuma jinjinawa al’ umman Kano a kan irin hadin kai da suka ba rundunar wajen zakulo bata garin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24

Ya kuma ce rundunar ’yan sanda ta jihar ba za ta lamunci duk wasu ayyukan ta’addanci da zanga-zangar da ta wuce gona da iri ba, domin a cewarsa rundunar a shirye ta ke wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar.

A gefe guda, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami'ai uku a kan kone ofisoshin 'yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel