Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda

Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya kori hadimansa na musamman da ke fannin tsaro

- Ya hada da wasu manyan jami'ansa uku sakamakon kone ofisoshin 'yan sanda da aka yi

- Gwamnan ya ce ya yi hakan ne saboda rashin kwarewarsu a fannin tsaron da ya saka su

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami'ai uku a kan kone ofisoshin 'yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar.

A wata takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin, Kenneth Ugbala, a ranar Lahadi, ya ce mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai, Nchekwube Aniakor da wasu shugabanni uku, ya sallamesu.

Shugabannin da aka sallama sun hada da Amos Ogbonnaya, Jerry Okorie Ude da Martha Nwankwo.

A wuraren ne 'yan daba suka kai wa ofisoshin 'yan sanda hari a Abakaliki, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Bata-garin sun tarwatsa wasu kayayyakin gwamnati ballantana na kan tituna a sassa daban-daban na jihar.

Ugbala ya ce gwamnan a kokarinsa na ganin tsaro ya tabbatar a jihar ne ya kori hadimansa, Premium times ta wallafa.

KU KARANTA: Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu

Gwamna ya fatattaki hadiminsa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda
Gwamna ya fatattaki hadiminsa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda. Hoto daga @PremiumTimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda

A wani labari na daban, Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya yi bayani dalla-dalla a kan dalilan da ke hassalar da matasa suna tada hankulan jama'a, asarar dukiya da kuma tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zangar EndSARS.

A ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba, yayin da Sanatan, kuma tsohon gwamnan, wanda yanzu haka shine mai wakiltar mazabar Imo ta yamma, ya yi hira da manema labarai a Abuja, inda yace mulkin kama-karya, zalunci, kunci, bala'i da yunwa ne dalilin da ya tunzuro matasa suka mayar da zanga-zangar EndSARS tashin hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel