Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

- Hukumar NAFDAC reshen jihar Kaduna ta bada muhimmiyar sanarwa ga wadanda suka kwashe abinci

- Kwamishinan yada labarai na jihar, ya tabbatar da cewa kayan abincin da magungunan suna dauke da guba

- An yi kira ga jama'ar jihar da su sanar da hukumomi wadanda suka kwashe kayan da kuma inda aka adana su

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) ta bada sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa kayayayyakin da aka kwashe daga ma'adanarta a yankin Narayi sun hada da magunguna masu tarin hatsari.

KARANTA WANNA: Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola

Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC
Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC - @vanguardngrnews
Asali: Twitter

"Duk wadanda suka sha wadannan maguungunan suna da yuwuwar kamuwa da manyan cutuka ko kuma mutuwa," kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

"Hukumar kamfanin abincin da aka kwashe musu kaya a ma'adanarsu da ke Kakuri sun tabbatar da cewa sun zuba wa masarar magunguna wanda hakan yasa ba zai yuw a ci ba,"

KARANTA WANNAN: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata

"A don haka ake shawartar mazauna jihar Kaduna da su kiyaye da abinci ko maganin da za su siya da kuma inda za su siya saboda hatsarinsu.

"Gwamnatin jihar Kaduna tana kira ga jama'a da su bayyana wadanda suka kwashe abincin da kuma inda suka boyesu domin gujewa hatsari," kwamishinan yace.

A wani labarin, Gwaman jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya sanar da cewa zai raba N500m ga 'yan kasuwar da bata gari suka balle masu shaguna ranar Juma'a a Ilorin, birnin jihar.

Ya ce wannan tallafin, na daga cikin kokarin gwamnatin jihar bisa jagorancin sa na ganin cewa ta taimakawa 'yan kasuwar wajen tsayawa da kafafuwansu.

Haka zalika, ya yi Allah-wadai kan yadda bata garin suka sace kayan sana'ar 'yan kasuwar, yana mai ba ta tabbacin cewa za a gano su tare da yi masu hukunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel